Connect with us

WASANNI

Ronaldo Ya Yi Wa Messi Fintinkau A Cin Kwallaye

Published

on

Bayan nasarar zura Kwallaye har 3 shi kadai a ragar Atletico Madrid a ranar Talata, yanzu kenan Cristiano Ronaldo na Portugal na da jimullar Kwallaye 124 a wasannin gasar zakarun turai inda ya dara takwaransa na Barcelona dan Argentina Messi da Kwallaye 18.
Haka zalika yanzu haka Cristiano Ronaldo ya wuce gaban Messi a nasarar zura Kwallaye 3 a wasa daya, wanda aka fi sani da (hat-tricks) a turance, inda ya yi makamanciyar nasarar har sau 8 a gasa daban-daban.
Bayan nasarar ta Jubentus kan Atletico Madrid a wasan na Talata, wannan ya nuna cewa, cikin shekaru 4 da suka gabata, ba a iya cire duk wata Kungiya da Ronaldo ke cikinta a gasar ta zakarun Turai.
Yayin da idan har Ronaldo mai shekaru 34 ya yi nasarar dage kofin na zakarun Turai a wannan karon kai tsaye ya kamo Francisco Gento dan wasan Real Madrid da ya kafa tarihin lashe kofin har sau 6 a tarihinsa na Kwallon Kafa.
A bara ne dai Jubentus ta amince da siyan Cristiano Ronaldo daga Real Madrid kan kudi fiye da yuro miliyan 99, a wani mataki na ganin Kungiyar ta yi nasarar lashe kofin a wannan karon, wanda rabonta da shi tun a shekarar 1996.
Ronaldo wanda ya lashe kofin zakarun turai sau biyar a tarihi guda hudu a Real Madrid sai kuma daya a Manchester United ya zura Kwallaye 24 cikin wasanni 36 daya bugawa Jubentus a wannan kakar ta bana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!