Connect with us

LABARAI

Rugujewar Bene A Legas: Dalibai 8 Sun Mutu, 37 Sun Tsallake Rijiya Da Baya –NEMA

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa, kimanin dalibai takwas ne suka rasu a wata makaranta da ake kira “Ohen Nursery and Primary School” da ke garin Legas sakamakon rugujewar benen da yara ke yin karatu a cikinsa, sannan kuma 37 sun tasallake rijiya da baya yayin da aka samu nasarar ceto su daga baraguzan ginin da ya fada musu a ka.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ta NEMA mai lura da shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye, ne ya tabbatar da afkuwar wannan lamari tare da bayyana adadin yaran da suka mutu da kuma wadanda aka ceto.
Ya kara da cewa, bayan faruwar wannan al’amari ne ba dadewa sai Daraktan Hukumar na sashin bincike da ceto ya bayyana a wurin, domin sa ido kan yadda ake gudanar aikin ceton. Haka kuma tawagar gwamnatin tarayya ta isa gurin domin gano yawan asarar da aka yi don a san yawan abuwan da suka kamata a kawo na agajin gaggawa.
Haka kuma ya ce, tawagar ta ziyarci asibitin da aka kwantar da wadanda suka ji rauni, domin ganinsu tare da yi musu jaje.
Zuwa yanzu an tabbatar da cewa, maza 17 da mata 22, wanda ya hada da malamai guda 2 da manya guda 3, sauran kuma duk kananan yara ne, su ne suka tsallake rijiya da baya.
Yayin da wannan bala’i ya wurin ya zama abin tausayi lokacin da iayayen suka fara barkowa suna ta koke-koke, kowa yana so ya san halin da dansa ke ciki, hattana iyayen ma da suka ga ‘ya’yan nasu su ma sun barke da kuka, babu mai jin muryar wani, duk wurin ya rude.
Wurin ya dada rudewa da kuka, lokacin da aka hako gawar wasu yara ‘yan biyu a cikin baraguzan ginin. Ganin wadannan yara ya sa wasu suka kasa daurewa dole sai da suka yi ta kuka, musamman ma mata. Ganin haka nan da nan aka saka gawarwakin a motar asibiti aka tafi da su Babban asibitin “Lagos Island” domin adana gawar tasu.
Wata mace wadda ta bayyana sunanta da Iya Ibeji, ta ce, ‘ya’yan kanwarta su uku Amina da Yusuf da Mubarak Oloyede na kwance a asibiti rai a hannun Allah.
Iya Ibeji ta ce, lokacin da uwar yaran, Ganiyat, ta samu wannan labarin ta garzaya zuwa asibitin, domin ta ga halin da ‘ya’yan nata ke ciki.
An zargi mai wannan gida da laifin cinkusa mutane a cikinsa, sannan kuma makotan wannan makaranta sun ce akwai sakacin Hukumara kula da gidaje ta jihar Legas da kuma karamar hukumar domin sun yi ta nuni ga hukuma kan cewa wannan ginin ya rube don haka yana iya faduwa kowane lokaci amma Hukumomin ba su dauki mataki ba duk da cewa sun zo sun gani kuma har sun sa masa jar lamba, amma har sai da wannan abin ya faru.
Makotan makarnatr sun ce tuni wannan ginin ya nuna alamun faduwa domin kuwa duk ya tsattsage, kuma an ce gina ya dade domin kuwa a kalla ya wuce shekara talatin ba tare da an yi masa wani gyara ba.
Kamar yadda wani makwabcin gidan Abdulazeez Elegushi ya bayyana cewa, “ sai aka gaya wa mai gidan, sannan kuma gwamnati tab a shi umarni ya gyara amma ya toshe kunnuwansa, ba mu san dalilin da ya sa ya ki bin umarnin hukuma, sannan su kuma suka ki matsa masa don ganin ya bi doka ba.”
Wani dan kabu-kabu Babajide Komolafe, da ke aiki a unguwar ta Ita-Faji, wasu daga cikin wadanda ke zaune a gidan sun fita lokacin Hukumar da ke kula da gidaje ta jihar Legas ta ce za ta rushe ginin.
“Akwai wasu abokaina guda biyu wadanda suka tashi daga gidan a cikin watan Nuwamba lokacin da kudin hayarsu ya kare. Suka lokacin mai kula da gidan ya matsa musu kan su sake biya domin su ci gaba da zama, amma suka ki yarda, saboda sun san hukuma ta yi wa gidan jan fenti cewa za ta rushe shi”.
“Na yi mamakin ganin cewa, an ce za a rushe gidan amma aka ki rushewa har sai da wannan abu ya faru, abin da muke tsammani shi ne, an hada baki da ma’aikatan ne suka kawar da kansu daga rushe gidan, sakamkon haka ga abin day a haifar,” in ji Komolafe.
Duk da cewa, ana takaddama a kan cikakken sunan makarantar, wani dan kabu-kabu da ya yi shekara uku yana aiki a unguwar ya tabbatar cewa, sunan makarantar “Ohen Nursery/Primary School”.
Wata da ke sayar da lemo da ayaba a unguwar, Bimbo Animashaun, ta ce, wannan abin da ya faru akwai sakaci a cikinsa, domin kuwa jami’an hukuma sun zo unguwar ta Ita-Faji, kuma suka umarci mazauna wannan gida da su fice su bar shi.
Domin kuwa yana daga cikin gidajen da aka yi masa jan fenti, za a rushe shi, amma suka yi burus da wannan umarni.
Haka ma wani dan tireda mai suan, Emeka Chukwuka, ya ce tuni gidan ya nuna alamar cewa, zai rushe, amma aka kasa daukar mataki har sai da ta kai ga ya rushe ya kuma yi barna mai yawan gaske.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!