Connect with us

MANYAN LABARAI

Sake Zaben El-Rufa’i Alheri Ne Ga Al’ummar Kaduna — Alhaji Abbas Likoro

Published

on

An bayyana sake zab en gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i da al’ummar jihar suka yi, babban alheri ne da zai zama mai amfani ga al’ummar jihar Kaduna da ma daukacin Nijeriya, baki daya.
Wannan furuci ya fito ne daga fitaccen mai tallafa wa al’ummar nan kuma shugaban al’umma da ke karakar hukumar Kudan a jihar Kaduna mai suna Alhaji Abbas Gambo Likoro, a tsokacin da ya yi a lokacin da ya zanta da manema labarai, kan sake zaben gwamnan da aka yi karo na biyu, a zaben da ya gabata.
Alhaji Abbas Likoro ya ci gaba da cewar, in an dubi yadda aka gwamnan Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a wasu kananan hukumomin jihar Kaduna da zaman lafiyar ta yi kamfa a shekaru da dama da suka gabata, wannan ma kawai, a cewarsa, ya dace al’ummar jihar Kaduna su fahimci El-Rufa’i ya ci gaba da mulkin jihar Kaduna babban alheri da ba zai misiltu ba.
A nanne Alhaji Abbas Likoro ya bayar da misali ga matsalolin tsaron da gwamna ke kokarin tabbatar wa, a shekaru da dama da suka gabata, a cewar Alhaji Abbas Likoro, ba a sami wani gwamna da ya dauki matakan da gwamna El-Rufa’i ya dauka ba, wanda zuwa yau, kowa a jihar Kaduna, ya san gwamna bai zura ido ga wannan matsala ta tsaro a kudancin jihar Kaduna ba.
Wadannan matakai da gwamnan ke dauka dare da kuma rana, babban alheri ne ga al’ummar Nijriya, domin duk lokacin da wata matsala ta taso al’ummomin da suke taso wadanda ke hanya daga wasu jihohi Nijeriya matsalar kan rutsa da su, wanda a wasu lokuta su kan sami raunuka wasu
ma su rasa rayukansu, wannan ya tabbata ba al’ummar jihar Kaduna kawai ke amfana da mulkin gwamnan jihar Kaduna, MalamNasir Ahmed El-Rufa’i ba ke nan.
Da kuma Alhaji Abbas Likoro ya juya ga ayyukan ci gaba da gwamnan ya fara da kuma wadanda ya kammala su, sai ya nanata cewar, musamman ayyukan da ya fara, da ya shafi ayyukan hanyoyi da bangarorin kiwon lafiya da ilimi dad a kuma farfado da masana’antun da suka durkushe, da kuma niyyar da ya fara aiwatar wa na samar da manya da kuma kananan masana’antu a jihar Kaduna, babban alheri ne da Allah ya tabbatar ma sad a wannan kujera karo na biyu zuwa shekara tya 2023.
A dai ganawar da wakilinmu ya yi da Alhaji Abbas Likoro, ya yi kira ga al’ummar kananan hukumomin jihar Kaduna 23,da su ci gaba da ba gwamna El-Rufa’i duk goyon baya da kuma addu’o’in da suka kamata, domin ya sami damar aiwatar da ayyukan da ya sa wa gaba, na ciyar da jihar Kaduna da kuma al’ummar jihar gaba a fannoni da dama da al’umma za su amfana da ribar dimukuradiyya, fiye da yadda suka samu a zangon farko da gwamna El-Rufa’i ya yi yana mulki.
Alhaji Abbas Gambo Likoro, ya kammala da kira ga ‘yan majalisar jihar Kaduna, tsofaffin ‘yan majalisar da kuma wadanda suka sami damar shiga majalisar a karon farko, da su ba gwamna El-Ruafa’i goyon baya da kuma sanya tunanin jihar Kaduna a zukatansu, kamar yadda gwamnan ke sa wa a shekara hudun da suka gabata, in sun yi haka, a cewar Alhaji Abbas Gambo Likoro, shi ne zai kara zama silar kara samun ci gaba a daukacin jihar Kaduna da kuma yadda sauran al’ummar Nijeriya su ma su amfana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!