Connect with us

LABARAI

Sha’aban Ya Bukaci Al’ummar Kaduna Su Ci Gaba Da Ba Gwamna Goyon Baya

Published

on

Tsohon dan majalisar tarayya da ya taba wakiltar Zariya da kewaye a majalisar kasa Honarabul Sani Sha’aban ya bukaci al’ummar jihar Kaduna da su ci gaba da ba zababben gwamna Malam Nasiru Ahmad El-rufa’i, domin samun cikakkiyar damar ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa da tallafa wa al’ummar jihar Kaduna.
Sanin ya wannan kalami ne jim kadan bayan sanar da cewa, Malam nasirun ya samu nasarar cin zabe karo na biyu a matsayin wanda zai ci gaba da zama gwamnan.
Ya ce, goton bayan da al’ummar jihar Kaduna suka bayar na sake zabar gwamnan ya tabbatar da cewa, sun gamsu da salon yadda yake tafiyar da gwamnatin tasa, saboda haka ne ma ya bukace su da su ci gaba bai wa gwamnan goyon baya.
Haka kuma tsohon dan majalisar ya yaba wa al’ummar Zariya da ma na jihar Kaduna baki daya bisa yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabi gwamnan karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!