Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sin Ta Fi Amurka Kawo Tasiri Ga Duniya

Published

on

Bisa sabon rahoton da mashahuriyar hukumar binciken ra’ayoyin jama’a ta kasar Amurka wato Gallup ta gabatar, kashi 34 cikin dari na jama’ar duniya sun nuna goyon bayan kasar Sin ta jagoranci duniya, amma kashi 31 cikin dari na jama’ar duniya sun goyi bayan kasar Amurka a wannan fanni. Sin ta sake zarce kasar Amurka wajen ba da jagoranci a duniya tun bayan rikicin hada-hadar kudi na duniya da ya abku a shekarar 2008.

An gudanar da binciken ra’ayoyin jama’a game da karfin jagorancin duniya na Sin da Amurka da Rasha da Jamus a kasashe da yankuna 134. Rahoton ya shaida cewa, a nahiyar Turai da Asiya da Afirka, yawan jama’a da suka fi nuna amincewa ga Sin ya fi na kasar Amurka a matsayin mai jagorancin duniya. Yawansu ya fi yawa ne a nahiyar Afirka, wato yawansu ya kai kashi 53 cikin dari.

Sanin kowa ne, sakamakon rikicin rancen kudi da Amurka ta gamu da shi ta fuskar sayen gidaje, ya sa duniya ta fara fama da mummunan rikicin kudi a shekarar 2008. Amma a wancan shekara, kasar Sin ta samar da matakan farfado da tattalin arzikin duniya da ma karuwarsa ta hanyar manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida da ta aiwatar har na tsawon kusan shekaru 30 da ma hazakar da jama’arta suka nuna. Haka kuma a wancan shekara, bisa kuri’ar binciken jin ra’ayin jama’a da Gallup ta yi, a karon farko an tabbatar da cewa, kasar Sin ta fi kasar Amurka tasiri a duk duniya.

Ya zuwa yanzu, bayan shekaru goma. Bisa taimakon da kasar Sin ta bayar, tattalin arzikin duniya ya farfado sannu a hankali, baya ga samun karuwa ba tare da tangarda ba. Amma wasu kasashe masu sukuni sun dauki lokaci mai tsawo ba su iya daidaita batun rarraba dukiyoyinsu yadda ya kamata ba, har ma lamarin ya haddasa tsanantar matsalar bambanci a tsakanin masu kudi da matalauta, da yawan basusukan da suka ci, da yawan masu rajin kare hakkin talakawa fiye da kima.

Yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauye da ba’a taba ganin irinsu ba a tarihi a duniya, kamata ya yi kasashen duniya su nemi ci gaba ta hanyar lumana, su kuma yi kokarin lalibo hanyoyi da damammakin da suka dace wajen samun bunkasuwa. A daidai wannan lokaci, al’ummomin kasashen duniya sun sake maida hankali kan kasar Sin.

A ’yan shekarun nan, kasar Sin na tsayawa kan wasu muhimman manufofin neman bunkasuwa, ciki har da yin kirkire-kirkire da bude kofa ga kasashen waje da neman bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba da sauransu, da tallafawa miliyoyin jama’a fita daga kangin talauci, tare kuma da kafawa kasashen duniya wani babban dandalin hadin-gwiwa dake kawowa juna moriya, wato shawarar “ziri daya da hanya daya”. Ya zuwa yanzu, akwai kasashe 123 gami da kungiyoyin kasa da kasa 29 wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin-gwiwa tare da kasar Sin a bangaren shawarar “ziri daya da hanya daya”, wannan ya zama ra’ayi mafi samun karbuwa a bangaren tafiyar da harkokin duniya tsakanin kasa da kasa.

Wani rahoton da kwalejin Brookings na Amurka ya fitar ya nuna cewa, jarin da kasar Sin ke zubawa a ayyuka daban daban da ake gudanarwa a fadin duniya za su iya share fagen bunkasuwar duniya baki daya. Rahoton ya ruwaito binciken da masana suka gabatar kan ayyuka 4300 da ake gudanarwa a kasashen duniya 138 wadanda kasar Sin ta saka jarinta a cikinsu, yana mai cewa, jarin da kasar Sin ta zuba ya amfanawa kasashen da aka gudanar da irin wadannan ayyukan.

Al’amuran sun shaida cewa, manufofin da kasar Sin ta gabatar game da “sabuwar huldar kasa da kasa” da “al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama” duk sun samu karbuwa daga kasa da kasa, sun kuma zama muhimmiyar ma’anar dake kunshe cikin jagorancin kasar Sin a duniya. (Masu Fassarawa: Zainab Zhang, Kande Gao, Murtala Zhang, Lubabatu Lei, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!