Connect with us

KASASHEN WAJE

‘Yan Bindiga Sun Harbe Masallata 40 A Kasar New Zealand

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Christchurch ta kasar New Zealand, ta tabbatar da faruwar harin ta’addanci akan wasu masallata a yankin Christchurch, da ake zargin wasu ‘yan bindiga ne suka aikata.

Rundunar ta tabbatar da mutuwar mutum akalla 40, inda ake tunanin wasu mutum 20 sun samu raunuka, zuwa yanzu rundunar ta tabbatar da kame mutum hudu da ake zargi.

Kwamishinan ‘yan sanda na yankin ya gargadi masallata da cewar kada su halarci wuraren ibada, saboda zuwa yanzu ba a san akwai barazanar harin ba ko babu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!