Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yan Bindiga Sun Kashe DPO Da ‘Yan Sanda 3 A Edo

Published

on

A daren ranar Talata ne, wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki ofishin ‘yan sanda da ke Afuze, ta karamar hukumar Owan ta gabas, Jihar Edo, suka kashe babban jami’in ‘yan sanda na wajen, DPO, insifekta guda da kuma wani mai mukamin sajent guda, gami da konstabul daya.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa wakilinmu cewa, maharan sun tsere da bindigogi da albarusai kafin su saka bam a ofishin ‘yan sandan.
An kuma ce, maharan sun kai irin wannan farmakin a ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ke garin, suka lalata kayan zabe suka kuma kone wata motar ‘yan sanda da ke wajen.
‘Yan sandan da aka kashe su ne, Supt. Tosimani Ojo, DPO na ofishin; Sgt. Justina Aghomon, wata mata mai ciki, Insifekta Sado Isaac da Kofur Glory Dabid.
Wani da lamarin ya auku a kan idonsa, Godwin Ikpekhia, cewa ya yi, a ranar ta Laraba da abin ya auku da misalin karfe 8 na yamma, a lokacin da yawancin jami’an ‘yan sanda da suke aiki a ofishin suka tafi ayyuka a waje.
“Mun dai ta jin harbe-harbe ne, amma ba wanda ya san abin da ke faruwa sai a safiyar Laraba.
“A nan take ne aka kashe DPO din da jami’an ‘yan sanda uku da suke a bakin aikin na su, a cikin ofishin.
‘Yan ta’addan ba su tsaya a nan ba kadai, sai suka nufi ofishin hukumar zabe ta INEC suka fara harbin kam mai uwa da wabi ga duk wadanda suka taras a wajen.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar ta Edo, Muhammaed [anmalam, wanda ya ziyarci wajen, ya ce za a fara gudanar da bincike ba tare da bata lokaci ba.
[anmalam, ya sha alwashin kama duk wadanda suke da hannu a kai harin.
“Za mu dauki matakai na gaggawa wajen hana ayyukan laifuka a yankin Owan, na Jihar.
Wakilinmu ya fahimci cewa, hare-hare a kan jami’an ‘yan sanda yana yawaita a wannan yankin na Owan.
A ranar 14 ga watan Yuli, na shekarar da ta gabata, an kashe jami’an ‘yan sanda hudu a wani wurin bincike da ke yankin, aka kuma kone gawarwakin su a cikin motar na su.
Hakanan, a ranar 23 ga watan Janairu, na wannan shekarar dan takaran jami’yyar APC a majalisar wakilai ta Jihar, mai wakiltan Owan ta Yamma, Mista Ohio Ezomo, an sace shi, sa’ilin kuma da aka kashe mai kula da lafiyarsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!