Connect with us

LABARAI

Yunkurin Babban Bankin Nijeriya Na Farfado Da Masaku Abin Yabo Ne

Published

on

Babban Bankin Kasar nan yana dab da fara aiwatar da wani shiri na farfado da masakun kasar nan wanda suna daga cikin manyan wuraren da suke samar da ayyukan yi. A shirin Bankin na baya-bayan nan na tsame kayan masana’antun saka daga jerin kayan da suke cin gajiyar musayar kudaden waje. Duk wadanda suke son shigo da kayan da aka sarrafa su a masakun na waje, suna da damar yin hakan, amma dai ba za su sami tallafin musayar kudin waje da gwamnati ke yi ba, sai dai su nemi ta su hanyar ta musayar kudaden domin shigo da kayan na su.
Saboda haka, wannan yunkuri na Babban Bankin Nijeriyar abin a yaba ne domin kuwa yin hakan na nuna cewa, Babban Bankin yana son ganin ya mayar da Nijeriya kasa mai gamsar da kanta da duk kayan da masaku ke sarrafawa ne. wannan matakin kuma ya kunshi bayar da tallafi ga masu noman Auduga na nan cikin gida yadda za su iya samar da Audugan da masakun ke bukata.
Daga cikin wannan shirin na Babban Bankin akwai bayar da goyon baya ga masu shigo wa da auduga matukar dai masu shigo wa da audugar za su samo irinsu na shuka ne daga nan cikin gida ya zuwa 2020. Haka nan, Babban Bankin duk dai a cikin tsarin da ya yi zai yi wani abu a kan samar da hasken lantarki ta hanayr samar da masakun a wasu wurare na musamman da ke cikin kasar nan da nufin farfado da ayyukan masakun domin samar da ayyukan yi.
Wannan a namu ra’ayin, wata hanya ce ta habaka hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyoyi daban-daban da nufin kuma bunkasa sashen aikin noma na tattalin arzikin kasa. Da zaran Gwamnan babban bankin kasar nan, Mista Godwin Emefiale, ya fara aiki, ya hango wata babbar kafa ta inganta ayyukan noma da nufin hanzarta fitar da kasar nan daga kamun da sashen man fetur ya yi wa kasar nan a matsayin babban hanyar tattalin arzikin kasar nan.
Wannan Jaridar za ta iya tunawa, Noma shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar nan har a jamhuriya ta farko bayan samun ‘yancin kan kasar nan, kai har ma a lokacin mulkin turawan mulkin mallaka. Noman shi yake samar da kudin da ake tafiyar da tattalin arzikin kasar nan. noman Cocoa, Auduga, Gyada da kwakwan manja wannan duk kadan ne daga cikin su, sune sune ginshikin tattalin arzikin na sassan kasar nan. amma abnin takaicin shi ne, duk wadannan abubuwan an yi watsi da su a lokacin da man fetur da iskan Gas suka bullo. Auduga a misali ta zama hanyar samun zuba jari a wancan zamanin, sannan kuma ta kawo bunkasar masaku na gwamnati da na ‘yan kasauwa a Legas da Kaduna da Asaba da Aba, wanda kuma wadannan masakun da suke tun lokacin mulkin Turawa ke bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Masu zuba jari daga kasar Asiya, su suka fi zuba jari a wannan bangare, wanda kuma a wancan lokaci masakun su suka fi samar da ayyukan yi a nijeriya fiye da kowane bangare in ban da gwamnatin tarayya. Yanzu haka, wandannan kasashen na Asiya sun koma sayo kayan da za su sarrafa a kananan masana’antunsu da ke Nijeriya daga kasashen waje. Manyan masakun da suke samar da tufafi a Nijeriya a wancan lokaci yanzu sun durkushe, wasu daga cikinsu ma an koma da wurin ya zama coci ko kuma wajen sayar da motoci. Babban abin bakin cikin dangahe da durkushewar wadannan masaku shi ne, rashin tabbata a kan kyakkyawan tsarin da ake da shi, da kuma bayar da kafar shigo da kaya daga wasu kasashe, domin samun sauki. Saboda haka ne muke ganin wannan yunkuri na Babban Bankin Nijeriya na farfado da masakun abin a yaba ne. Duk da haka muna kara kira da babbar murya ga Babban Bankin, cewa ya kara zage dantse wajen aiwatar da wannan kyakkyawar manufa ta sa, domin kuwa akwai masu yi wannan yunkuri zagon kasa, saboda irin amfanin da suke samu daga durkusheawar masakun na Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!