Connect with us

KASASHEN WAJE

Badakalar Daukar Dalibai Mafi Girma A Amurka

Published

on

An gurfanar da wasu shahararrun mutane 50 a gaban kotu, saboda wata badakala mafi girma ta bada kudi domin shiga wasu manyan makarantu a Amurka.
Wasu fitattun ‘yan Hollywood, da kococin kwalejoji, da masu kula da daliban da ke rubuta jarabawa da kuma wani babban jami’in wata kwaleji, na daga cikin mutane 50 da ake zargi a wani abin da masu gabatar da kara su ka kira, babbar tabargazar daukar dalibai da bangaren shari’ar Amurka ya taba gani.”
Dalibai kan samu shiga wasu sanannun makarantu, bayan iyayensu sun bayar da cin hanci ga wani William Rick Singer, don shirya jarabawar bogi, ya samar da takardun kammala jarabawa na bogi da kuma samar da takardun cimma wasu nasarori na bogi a fannin wasannin motsa jiki.
Wannan bayanin na kunshe cikin sanarwar da fannin Ma’aikatar Shari’a ta bayar, a wani taron manema labarai jiya Talata da kuma wasu takardun kotu da aka sake ga jama’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!