Connect with us

TATTAUNAWA

Gudummowar Farfesa Ibrahim Garba Ta Bunkasa Tsaro A Jami’ar Ahmadu Bello

Published

on

KANAR JIBRIN TUKUR (Ritaya) kawrarren jami’in tsaro da ya harci yake-yake a kasahe daban-daban domin kare martabar kasar nan, yanzu haka kuma shi ne baban jami’in tsaro na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a tattaunawarsa da Edidatanmu SABO AHMAD KAFIN-MAIYAKI, ya bayyana sababbin dabarun da suke amfani da su, wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukoyoyin al’ummar wannan jami’a da ma dukkan rassan jami’ar da ke wasu wurare. Haka kuma ya nuna irin goyon bayan da sashin tsaron ke samu daga shugaban jami’ar, Farfesa Ibrahim Garba. Ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:Masu karatunmu za su so ka gabatar da kanka.
Sunana Kanar Jibrin Tukur (Ritaya), ni ne shugaban sahin tsaro na jami’ar Ahmadu Bello, kuma ne kula da tsaron dukkan wani sashi da ke karkashin jami’ar Ahmadu Bello a ko’ina yake a fadin kasar nan.
Loakcin da ka zo wannan jami’a ya ka same ta a fannin tsaro?
Na zo na same ta cikin tsari mai kyau na tsaro, domin kuwa ita wannan jami’a tana da tsaro tun da fari, shi ya sa ma cikin ikon Allah muka samu nasara dukkan barazar da aka fuskanta a baya dangane da matsalolin tsaro a wannan kasa da wasu makarantu Allah ya kiyaye mu.
Da yake ka zo wannan jami’a a daidai gabar da al’ummar kasa ke cikin fargaba a kan harkar tsaro wane tanaji ka kara yi domin ganin cewa ka dora a kan yadda ka same ta domin tabbatar da tsaron a wannan lokaci?
Kamar yadda na ce bisa cikakken goyon bayan da muka samu daga shugaban jami’a na samu nasara kirkiro wasu sababbin dabaru wadanda suke taimaka wa wajen tabbatar da tsaro. Wato babban abin da tsaro ya kunsa su ne, kare lafiyar al’umma da dukiyoyinsu da kuma daidaita tsakaninsu idan akwai matsala sannan kuma da samar da yanayi mai kyau, yadda hankalin al’umma zai kwanta su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare fargaba ba.
Lokacin da muka zo akwai rahotanni na satar mota da daga lokaci zuwa lokaci ake yi a wannan jami’a. Hanya ta farko da muka bi wajen hana wannan satar ita ce, duk wanda zai shigo da mota daga get za a ba shi shaida, sannan idan ya je wurin da zai ajiye motar nan ma sai an ba shi wata shaidar, kuma ba zai fita da wajen fakin din ba sai ya bayar da shaidar da ka ba shi, sannan kuma in ya je get nan ma sai ya bayar da wadda aka ba shi, sannan ya fita.
Wannan tsari da muka kawo, ya kawo karshen satar mota a wannan jami’a. Domin tun da aka fara wannan tsari ba mu sake samun wani rahoto ba na satar mota, wannan ta tabbatar da cewa, mun samu nasara ta wannan fuska.
Sannan mun daura damarar yaki da kungiyoyin asiri ta hanyar hada kai da dalibai wadanda suka taimaka mana wajen zakulo dukkan wani dankungiyar asiri, hakan dam ka yi shi ma ya sa an kawo karshen wannan matsala a wannan makaranta.
Bayan wanna mun tanaji katin shaida ga dukkan wanda ke zaune a wannan makaranta wanda shi ba daliba ba ne kuma ba ma’iakcin wannan jami’a, domin mu tabbatar da wadanda ke cikin jami’ar domin kada bata-gari su samu mafaka, saboda mun san duk wanda ke zaune a cikin wannan jami’a yana da izinin zama, kuma sa ido sosai wajen tattace wa kafin mu ba mutum wannan izinin zaman.
Haka kuma ga dukkan wadanda ke gudanar da harkokin kasuwanci a wannan jami’a su ma mun ba su katin shaidar zamansu a harabar jami’ar.
Kasancewa jami’ar Ahmadu babban wuri ne wadda ta yi iya da daji a wasu bangare, ta ya ya kuke tabbatar da tsaro a irin wadannan wurare?
Da ma akwai tanajin da aka yi na tsaro a irin wadannan wurare ta hanyar samar jami’an tsaro wadanda ake ce musu “Hunters” ko maharba, suke kula da irin wadannan wurare da muke da su.
Sannan kuma mun tanaji kananan Babura za ake yin faturu da su, jami’anmu na zagaya wa domin tabbatar da cewa, komai lafiya, wannan ma ya taimaka mana wajen samun tsaro a kan irin wannan iyakoki. Domin kuwa da zarar wani bata-gari ya yi yunkurin shigo cikin wannan jami’ar ta irin wadannan hanyoyi, jami’anmu za su damke shi tun kafin ya kai ga shigo. Saboda mun kama masu irin wannan mugun nufin kuma mun mikasu ga ‘yan sanda.
Ya ya dangantakarku take da makwabtan wannan jami’a?
Muna da kyakkyawar dangantaka tsakaninmu da makwabtanmu da sarakuna da kuma masu unguwanni, domin kara kulla wannan dangantakar ce ma dukkan abin da ya taso a wannan jami’ar mukan tsoma su ciki. Muna ba su dama iadan za a dauki ma’aikata su kawo mutanensu, yadda su ma za su amfana da kasancewa makwabtan jama’a, kuma suna jin dadin haka, don haka suke ba mu cikakken goyon baya wajen ganin an samu tabbataccen zaman lafiya a wannan jami’a.
Wane kalubale kuke fuskanta ta fuskar tsaron jami’ar?
Kusan zan iya cewa, babu wani babban kalubale, sai dai kawai ‘yar matsalar da muka iya fuskanta a wasu iyakon jami’ar musamman ta wajen daji-dajin nan, amma shi ma mun ci lagon wannan matsalar.
Me yake faranta maka rai a matsayinka na shugaban sashin tsaro na jami’ar Ahmadu Bello?
Babban abin da ke faranta min rai shi ne yadda muke zaune lafiya, babu fargaba, kowa na walwalarsa kamar yadda yake bukata. Sannan kuma ina jindadi bisa cikakken goyon bayan da nake samu daga ma’aikatana da sauran ma’aikatan jami’a da dalibai da kuma mai gayya mai aiki shugaban jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Ibrahim Garba.
Wane sako kake da shi ga mahukuntan wannan jami’a?
Sakona gare su shi ne su ci gaba dab a harkar tsaro goyon baya kamar yadda suka saba, domin kuwa da irin wannan goyaon bayan ne muka samu wannan nasarar da muke gani a halin yanzu. Sannan ga su kuma dalibai su ma suna da gudummowar da za su bayar wajen tabbatar da tsaro, haka ma dukkan masu zama da makwabtan wanna jami’a kowa na da irin gudummowar da zai bayar wajen samun ci gaban tsaro a wannan jami’a. kuma muna godiya da gudummowar da suke bayarwa a halin yanzu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!