Connect with us

SHARHI

Me Ya Sa Suka Tsani Gwamna Ganduje?

Published

on

Tun lokacin da aka dage zaben gwamnoni a wasu jihohin kasar nan, na himmatu tare da bibiyar halin da ake ciki a siyasar wannan kasa da abin yake tafiya yana dawowa, musamman da yake hankulan masana siyasa sun fi karkata jihar Kano, inda ake fafatawa da Gwamna mai ci, Dakta
Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC, da kuma Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP, wanda ake ganin Kwankwaso ya kakabawa al’umma don ya samu damar holewa idan sun kafa gwamnati.
Hakika yadda mafi yawan mutane suke kallon lamarin sam ba haka yake ba, jam’iyyar APC a matsayin ta na mai rike da madafun ikon, ta tsaya tsayin daka don ganin an yi zabe ma nagarta, ko ba komai, hakan zai shiga tarihi cewar karkashinta aka gudanar da sahihin zabe a Nijeriya,
yayin da PDP wadda ta yi kaurin suna wajen magudi, ta yi kokarin yin amfani da damar sakwakwan da APC ta yi don cin karenta babu babbaka.
Mu gan irin aringizon kuri’un da ta yi Kano, tare da yin barazana ga jami’an zabe kan lallai sai sun ayyana dan takararsu a matsayin wanda ya lashe.
Babban abin tashin hankalin shi ne, yadda aka rika sauya hakikanin abubuwan da suka faru ta hanyar gurbata zance, rahotannin karya da sharri da ake yada wa kan Gwamna Ganduje sun yi yawa matuka da gaske.
Sai dai har yanzu alkaluma sun gaza yin rubutu, bakunan sun gaza ci gaba da batu, shafukan jarida sun gaza kawo hakikanin dalilin da ya sa tsagin tafiyar Kwankwansiyya suke so ko ta halin kaka sai sun ga bayan Gwamnan Jihar Kano Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ko suna
bakin cikin da ayyukan alherin da yake yi ne oho.
Balahira iya balahira, bahallatsa iya bahallatsa, duk wata sukuwa da za su yi sun gama, karshe suna tsamewa a hankali suna faduwa kasa warwas. Mufakkirai sun yi batu kala-kala irin ci gaban da jihar Kano ta samu karkashin mulkin Gwamna Ganduje, amma tawagar ‘yan son zuciya
sun gaza fahimta, sun dage lallai ilalla sai sun ga bayansa domin cim ma mummunar manufarsu.
A zahirin gaskiya, su ne ke zuluntar Gwamna Ganduje, amma sai su fito kafafen sadarwar zamani suna kwakwazon an zalunce su. Babban abin da suke son cim ma shi ne, dakushe hasken manyan ayyukan da Ganduje ya yi wa Kanawa domin su sake zabensa ya ci gaba.
Tsakanin labaran karya da PDP a jihar Kano sun zama dan juma da dan jummai, tare suke tafiya kafada da kadafa. Suke yunkurin yin magudi, amma sai su fito suna kwarmaton za a zalunce su. Kowa ya san me doka ta tanada game da gudanar da zabuka, amma Kwankwasawa sun toshe
kunnensu, kowace riba suke samu daga yada labaran karya oho?
A halin da ake ciki yanzu, kididdiga tana nuna cewar Gwamna Abdullahi Ganduje zai sake lashe zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da hammayya ba, hakan za ta iya yiwuwa ne sakamakon sauyin da a kullum siyasar Kano ta ke samu.
Dakta Abdullahi Umar Ganduje mutum ne haziki da ya dace jama’ar Jihar Kano su goyawa baya, kasancewar gamo-da-katar da suka yi na wannan dan ta’aliki da ya amsa tayin da aka yi masa na tsayawa takarar kujerar gwamnan Kano karkashin inuwar tutar jam’iyyar APC canji, wadda a Kano ya dace mu ce mata DORI, domin kuwa kisan mummuken da aka so yi wa jihar, ya zo domin yin manyan ayyukan da al’umma za ta amfana, shi ya sa ma ake masa lakabi da Ganduje Gandu Aiki.
Idan muka yi la’akari farin jini da Gwamna Ganduje yake samu daga wurin Kanawa daga lokacin daka dage zaben zuwa yau, lamari ne da za a duba, kuma hakan ka iya bashi kuri’u fiye da yadda abokan hamayyarsa ke tsammani.
Duk wasu alamu na lashe zabe da Gwamna Ganduje ka iya yi kullum kara bayyana suke yi, musamman irin salon siyasar da ya dauka na yafiya da tuntubar dukkanin wadanda ya san za su bashi goyon baya.
Dakta Abdullahi Umar Ganduje, mutum ne mai yafiya, sam ba shi da rikon mutum a rai, ko da kun samu sabanin a baya, matukar ka nuna sha’awarka na shiryawa, Gwamna ba ya kasa a gwiwa wajen yafewa. Idan hali ya yi, da kansa yake takawa har kofar gidan mutum domin su gaisa, wannan ya kara bayyana dattakon mai girma Gwamna Ganduje karara. Duk irin zaluncin da tsagin Kwankwasiyya yake yi masa, babu ruwansa, lissafinsa kwaya daya ne, yadda zai ci gaba da ayyukan alheri ka Kanawa.
Sabanin Madugun tafiyar Kwankwasiyya, wanda kullum yake siyan fili a gidajen rediyo, ya ci mutuncin masu mutunci, ya zagi gwamna, sarakuna da malaman addini.
Kanawa sun yi mamaki irin yadda Gwamna Ganduje ke cigaba da shimfida ayyukan alheri, duk da irin kalubalen da yake fuskanta na adawa da tarnaki daga bangaren Kwankwasiyya.
A cikin halayensa, bai damu da kallon tasirin adawar ba, ya fi mayar a hankali wajen runtumo ayyukan da al’umma za ta amfana, walau wadanda ya kirkiro ko kuma wadanda ya
gada.
Duk da adawa da wasu ‘Yan siyasa sana’a ke wa Ganduje, duk mutumin da zai yi adalci ya san cewa mai girma gwamna na iya bakin kokarinsa, matsayinsa na mutum, domin ayyukan da yake karasawa tare da shimfida sabbi, ko wadannan jihar Kano ta samu a mulkin Ganduje kamata ya yi a gode wa Allah ganin yadda Nijeriya ke fama da matsalar tattalin arziki.
Babu mamakin Kwankwasawa suna hassada ne saboda an dauko hanyar shafe tarihin ayyukan da suka gudanar lokacin da suke kan gwamnati.
Gadar sama wadda ta faro daga Fagge ta wuce ta ‘yan Kura da Kasuwar Sabongari aiki ne da in ba Gandujen ba ba wanda zai ci gaba da wannan aiki don wannan ita ce gadar saman da tafi kowacce tsaho a Afrika ta Yamma kuma Kwankwaso ne ya faro aikin in ba Ganduje ba?
Bangaren ilimi ma Ganduje ya kokarta sosai don zamaninsa makarantun sakandire a Kano dalibai suka samu saka samu sakamakon da an fi shekaru 7 ba a samu irin sa ba. Haka zalika gwamnatin Ganduje ta mayar
da malaman wacin gadi da Kwankwaso ya samar, wadanda ba su san madogararsu ba.
Bisa dukkanin alamu ya nuna cewa mutanen Kano lokaci kawai su ke jira domin sake zaben Dakta Abdullahi Umar Ganduje a karo na biyu domin ya dora da ayyukan ci gaban a jihar Kano.
Ko bako ne ya zo Kano ya kalli manyan ayuyukan Gadar Kofar Ruwa da ta hanyar Panshekara da kammala ta Sabon Gari wadda tsohuwar Gwamnati ta fara ba ta kammala bam ga kuma ayyukan kammala gina katafaren ginin asibitocin Zoo Road na Kalifa Ishak Rabi’u da na Giginyu na Muhammadu Buhari da sauran tituna birnin Kano da kawaye da kuma ayyukan hanyoyi da a ka yi a yankunan karkara da dai sauran aikace-aikace na cigaba da a ka samu a kananan hukumomi 44 na Kano da horar da dubban daruruwan matasa da mata sana’o’i da basu jari da kuma inganta harkar lafiya, ruwa, tsaaro da sauran duk abubuwa da ba za su lissafu ba, ya nuna cewa gwmanan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje na yi wa Kano da Kanawa
ayyuka domin cigabansu, wadannan da ma wasu tarin ayyuka da gwamnatin Ganduje ke yi, sunya Kanawa suna alfahari da shi, har ila yau sun shirya domin sake zabarsa a watan Maris mai kamawa.
Jihar Kano ba ta taba cin karo da gwamna tamkar Abdullahi Umar Ganduje ba, domin ya sadaukar da lokacinsa wajen ganin duk manyan ayyukan da ake aiwatarwa a Kanon wadanda za su taimaki talakawa ne.
Duk wanda zai yi wadannan ayyukan cikin shekaru hudu a matsayin gwamna, lallai akwai
bukatar al’umma su sake ba shi dama a karo na biyu domin ya dora daga inda ya tsaya. A yanayin tafiyar siyasar Kano, Kanawa sun karbi Ganduje dari bisa dari, maza, mata da matasa baki daya sun amshi kiran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, lokacin da ya daga hannun Ganduje, ya kuma umarci Kanawa da su zabi Gandujen Kanawa a matsayin Gwamna. Masu
mugunyar tunani ne ke sauya akalar zance domin biyan bukatarsu ta kashin kai.
Babu abinda ya dace ga Kanawa, musamman a wuraren da za a sake zabe da ya wuce fitowa kwansu da kwarkwata don karasa ladansu na zabar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Khadimul Islama, a karo na biyu. Mubarak Umar Ya rubuto daga Kano
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!