Connect with us

NAZARI

Yadda Rubabben Tumatir Ke Haddasa Cutar Kansa

Published

on

Hausawa suna cewa, ‘Lafiya Jari, amma sau da yawa, in mutum bai yi hankali ba, abin da zai ci domin neman lafiyan yakan iya gurbata masa rayuwarsa. Wani abin da muke ci domin ya baiwa jikinmu lafiya, yana iya sanya cuta a cikin jikin namu, matukar ba mu ci shi ta hanyar da ta dace ba.
Duk abin da muke ci, shi yake alamta yanayin lafiyar da za mu samu a jikinmu, ko dai ya yi mana magani ko kuma ya zama cuta a jikin namu, tilas dayan biyun nan ne!
Tumatir abu ne mai matukar amfani a jikinmu, duk ta yanda aka sarrafa shi. Da wahala ka sami al’umman da ba sa amfani da Tunmatir a abincin su ko abin shan su na yau da kullum. Masana sun ce, tumatir sinadari ne babba wajen kare mana hanyoyin jinin cikin jikinmu kar su lalace. Tumatir din kuma yana dauke da sinadarin Lycopene, wanda yake taimakawa wajen rage mana hadarin kamuwa da cutar kansa. Kamar kuma yanda lafiyayyun tumatir din suke amfanar jikin namu, suna kuma iya zama masu hadarin gaske ga jikin namu in muka ci tumatirin da ya rigaya ya rube.
Sau da yawa zaka ga ana siyar da Tumatirin da ya rube da arhan gaske, irin su ne zaka gansu sun yi laushi sosai har suna digan ruwa saboda rubewa. A wasu lokutan sukan rube su yi tauri, saisu kasance gida ga tsutsotsi da sauran kwari, wadanda sukan yi kwayayen da za su iya haddasa cutuka daban-daban in an ci su.
A watan Satumba, 2018, hukumar kula da lafiyar abinci da abin sha ta kasa, (NAFDAC), ta gargadi ‘yan Nijeriya daga cin tumatirin da ya rube domin su tsira daga kamuwa da cutar kansa. Mataimakiyar daraktan hukumar, Christiana Essenwa, wacce itace ta bayar da gargadin tana cewa, “Da zaran tumatir ya rube, za su kasance akwai cutar microorganisms, a tare da su, wanda cutace mai hadarin gaske, sukan kuma iya haifar da cutan kansa. Sukan kuma karya garkuwan jiki ga maza da kuma dabbobi, wani binciken ma ya tabbatar da suna iya lalata hanta.
A cewar ta, wasu mutanan suna ganin cewa wai ana iya cin rubabben tumatir a bayan an wanke shi an kuma dafa shi, amma sai ta tabbatar da cewa, su wadannan cutukan da ke cikin jikin rubabben tumatirin, ba sa mutuwa a sabili da an wanke su ko an dafa su, zafi ba ya kashe su. don haka ta gargadi al’umma daga cin rubabben tumatir wadanda su ne mafiya arha a kasuwa, tana mai cewa, zai fi kyau ka kashe kudi wajwn tsawaita rayuwarka, a maimakon ka sayi mutuwarka da kudin ka.
Cutukan da ke tattare da cin rubabben tumatir suna da yawa, sannan kuma ba wai nan take daga an ci su ne ake mutuwa ba, sannau a hankali ne suke yin kisan. Sannu a hankali, manyan bangarori hudu na jikin mutum (hanta, koda, mafitsara da fata) sukan kamu, daga nan sai tsarin garkuwan jikin mutum ta daina aiki.
Wasu daga cikin masusiyar da tumatir sai su ce maka, ai ba duk tumatirin da ya yi laushi ne ya rube ba, saboda wasu suna yin taushi ne saboda sun fado sun fashe, a lokacin da ake kawo su kasuwa daga gonaki. Hakan da gaske ne, sai dai yana da mahimmanci a fahimci cewa, ai a lokacin da suka fadi suka fashe ne kuma kudaje da sauran kwayoyin cuta suke samun kafar shiga cikin su domin su lalata su.
Ya kamata mu kula sosai da irin tumatirin da muke saye tun kafin mu kai ga yanyanka su ko nika su ko kuma mu sha su kai tsaye. Tilas mu kula duk tumatirin da ya kwashe kwanaki masu yawa zai iya rubewa ba tare ma da ya yi laushi ba. Don haka, kar mu ci irin wannan tumatir din.
Duk tumatirin da ya rube, tabbas yana da hadarin gaske a tare da shi in an ci shi. Don haka, ya kamata mu gargadi mutane musamman ma mata da su guji siyan tumatirin duk da ya rube domin a ci.
Domin neman kare kanmu daga kamuwa da cutar Kansa, sai mu guji cin tumatirin duk da ya rube.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!