Connect with us

HAYAKI

Watsi Da Mutane Ya Dakushe Farin Jinin Siyasar Gwamna M.A Abubakar A Jihar Bauchi

Published

on

Tun daga lokacin da gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya samu nasarar hawa karagar mulkin jihar Bauchi na daya daga cikin gwamnoni da suka yi farin jini a idon mutanen jihar Bauchi saboda kasancewar tsohon gwamna Malam Isa yugudu ya kudiri aniyar dora Alhaji Auwal jatau a matsayin gwamna duk da cewa mutane sun nuna basu gamsu da wannan zaben gwamna ba saboda akwai mutanen da ake ganin idan su aka kawo za a fi samun nasara
Wannan dauki dora da Malam Isa ya so yi yasa bai samu nasara ba kuma ya rabu da mutane dutse a hannun riga haka shima Muazu ya yi a lokacin Nasara Umar. Don haka duk da irin fadi tashin da akayi ta yi Mohammed Abdullahi Abubakar ya samu nasara har ya lashe zaben gwamna duk da cewa bai jima a cikin jamiyyar APC ba. A madadin hawansa kujerar gwamna ke da wuya ya kasance ya jawo mutane jikinsa yana neman shawarar da ta dace, sai bai yi haka ba ya ci gaba da fantamawa har ya jima Kafin ya nada kwamishinoni lamarin da tun daga lokacin mutane suka fara tsinkewa da shaaninsa game da yadda yake son kudi da rains mutane har Wanda suka masa wahala. Kuma yana nuna bai damu ba idan mutane sun barbtafiyarsa.
Musamman ganin ya gaji gwamnatin Isa yuguda mai kyauta da nada mutane kan mukamai da suka hada da kwamishinoni da masu ba gwamna shawara kala kala kuma ya dauki mutane masu yawa aiki musamman a fannin koyarwa da asibitoci, Wanda da bai dauki aiki ba da ba a san matsalar da za a shiga ba saboda rashi ko karancin maaikata wanda a halin yanzu yawanci ofisoshin gwamnati an rufesu.
Misali akwai ofishin maaikatar ayyuka da sufuri a Bauchi da Azare da gidajen gona a nabordo da Miya da Azare da Bauchi a baya ko ina akwai maaikata kusan dubu ko sama da dubu amma yanzu wasu sun mutu wasu sun yi ritaya babu ofishin da ke da Mutum dari da makamancin haka.
Saboda tunanin gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar kullum shine ina zai yi tsimin kudi ko ina zai samu kudi lamarin da ya sa shi kafa kwamitin bincike kala kala da nufin nemo kudin da aka sace. Akwai babban kwamitin airkwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa, a matsayina na dan jarida na bi kwamitin wurare da dama amma na lura duk inda aka je za a samu anyi aiki saiko ace yayi tsada musamman wata makaranta da muka je a garin yuguda da wani asibiti kowa ya San an yi aiki. Haka jamiar jihar Bauchi da Tatari Ali polytechnic da filin jirgi da asibitin Bacas da asibitoci Sama da a shirin da gwamna yuguda ya gina a kananan hukumomi da ayyukan hanya a cikin gari da yankunan karkara Wanda duk kin Allah Mutum bai isa yace yuguda da Muazu basu yi aiki ba a jihar Bauchi. Amma Mohammed Abdullahi Abubakar ya kasa samar da kudi ko kula da ta dace game da ayyukan ya gada don a lura da su.
Amma duk da wannan ayyukan da gwamna Mohammed Abdullahi ya iske bai dora nasa fiye da nasu ba saiko maganganun anyi wa dukiyar Bauchi cin kaca a kullum amma shi bai dauki maaikata ba kuma bai iya rike maikatun gwamnatin ba saiko a kafa kwamitin bincike inda mutane dattijai suka yi ta mutuwa a layin tantance maaikata da yan fansho an kai wani matsayin da mutane suka yi ta laantar yadda ake bincike kuma daga karshen babu wani sakamakon da aka samu na maaikatan bogi ko cin dukiyar gwamnati.
Na gamu da kwamanda Baba Gamawa a ranar da akace an dawo da jirgin jihar Bauchi a filin jirgi daga nan ya bukaci na rika zuwa ina taya shi yayata manufar kwamitin inda muka rika shiga da fita wurare. Amma ganin yadda yake zagewa wajen aibanta mutane cewa sun yi sata ko almundahana, wata rana muna tare na bashi shawarar nace ya bi Bauchi a hankali kar ya rika hawan kawara wa mutane zasu kai shi su baro saboda na fahiamci gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ba zai kai shi tudun mun tsira ba. Daga nan na bashi shawarar idan zai yiwu ya nemi aiki a sama ya tafi shine mafi alheri. Nayi mamakin yadda Baba Gamawa ya dauki shawarar da na bashi har yakan kirani nazo mu gaisa mu yi hira duk da matsayin sa da girmansa amma ba shi da girman kai. Wata rana sai ya kirani yace ya samu wani aiki a sama na masa fatar alheri kuma har yanzu muna tare yana zuwa gidana INA zuwa gidansa.
Tunda gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya fara rabuwa da su Baba Gamawa sai su Sanin Malam da wasu manyan hadimansa kwamishinoni da yan siyasa. Saboda irin manyan mutanen da ya rabu da su sai suka share masa hanyar rabuwa da mutanen kirki da suka masa wahala suke dorashi hanya ta Kirki. Daga nan sai na ji an kwaso wasu mutane ana zuba wa a gidan radio suna fadin karya da gaskiya wai sune masu kare muradun gwamnati. Daga bisani mutanen Kirki da dama sun bar gwamnatin yadda kowa ke neman abinci da zai ci ta kowane hali, inda suke rantsuwa a gidajen radio kan karya da nufin kare muradun gwamna.
Bayan haka Mohammed Abdullahi Abubakar idan ya Nada kwamishinoni watanni kadan sai ya sauke su ya bar gwamnatin tana lilo hannun manyan sakatarori. Akwai kwamishinoni da mukayi aikin raba kayan plann international dasu a BSADP an kaddamar da motoci da kayan kiwon lafiya da odfam suka ba jihar Bauchi, an gama kenan da yamma kwamishinoni sun zauna gaban talabijin ganin labarin sai suka ji sanarwar an sauke su haka aka bar gwamnatin tsawon watanni Kafin aka Nada kwamishinoni. Wani kwamishinan da jinin sa ya Hau har Yau yana jinya.
Bayan haka akwai lokacin da shugabannin kananan hukumomi suka hadu a Dass wai suna share wajen da Barista dogara da mutanen sa suka yi taron fara aikin hanya da gwamnatin tarayya ta shirya yi amma washe gari sai aka sauke dukkan shugabanni na kananan hukumomi sai kwanaki aka sake nadawa.
Irin wannan rashin tabbas da wulakanci suna sa yan siyasa taka tsantsan da gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar inda duk Wanda ya shiga gwamnatin sai ko ya fara tunanin me zai samu idan babu sai ya kama gaban sa ko ya koma adawa. Don haka ko ni akwai lokacin da tun Kafin a rantsar da Barista Mohammed Abdullahi Abubakar a matsayin gwamnan jihar Bauchi akwai manyan yan siyasa da suka kaimu gaban sa a gidan maitama yadda ya zauna kan cewa suna son nazo a yi gwamnati dani tunda ban yi gwamnatin yuguda ko Muazu ba. Amma da na fiskanci lamarin gwamnatin bayan rantsar da ita na nuna ci gaba da harkokin irin na aikin jarida da kasuwancin da nake sun fi alheri a gareni.
Ya zuwa wannan lokacin mutanen da suka nemi na zo a yi dani basa gwamnatin sai Mutum daya ke rike da wata hukumar ta jeka na yika. Wannan daili yasa mutane da dama sun Kauracewa tafiyar gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar har lokacin da aka zo wannan zabe inda yake ganin ta kowane hali zai ci zabe sai ko aje ayi ta fama a kotu alhali yanzu kan mutane ya waye sosai. Sai wani lokacin zan ci gaba da wannan rubutu har na kawo lalilai a kalla 20 da suka kawo dakushewar siyasa Mohammed Abdullahi Abubakar a jihar Bauchi kuma ya kamata idan Allah ya tabbatar wa Sanata bala Mohammed wannan kujerar ya kamata ya kiyaye su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!