Connect with us

SIYASA

Al’umma Mazabar Gama Sun Jaddada Goyon Bayansu Ga Gwamna Gaduje

Published

on

Al’ummar Mazabar Gama daya daga cikin mazabun da za a sake zaben Gwamna ranar Asabar 23 ga watan Maris na shekara 2019 sun gayyaci Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya je domin su bayyana masa goyon bayansu a zaben mai zuwa. Dubun dubatar mutane ne suka tare shi tun daga Bompai har zuwa Kwanar Tudun Wada zuwa Gama wanda ta kunshu Gama A,B,C da Gama D da kuma Gama Fuani da Gama Barbari.
Sabodayawan dimbin Jama’ar da su ka tari Gwamnan ya sa sai da Gwamnan ya kwashe sama da awa hudu yan kewaya mazabar ta Gama, Saboda haka Gwamna Ganduje sai ya yi masu godiya saboda zaben da suka fito su ka yiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na boyu, haka kuma ya gode masu sakamakon fitowa da su ka yi lokacin zaben Gwamna wanda ba a kammala ba.
Gwamna Ganduje ya ce, muna yi maku godiya saboda namijin kokarin da kuke yi wajen zabenmu, sanin kanku ne cewa lokacin zaben Gwamna da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano, ‘yan Jam’iyyar adawa ta PDP sun yi aringizon kuri’u tare da tafka magudi. Wanda hakan ne ya sa Hukumar zabe ta kasa ta soke zabukkan a wasu wurare wanda za a sake a wannan Asabar mai zuwa.
Saboda haka sai Gwamna Ganduje ya yi kira da su sake fitowa kwansu da kwarkwata domin sake jefa masa kuri’a saboda ya ci gaba da yi masu ayyukan raya kasa da kuma tallafawa rayuwar al’umma. Matasan mazabar ta Gama sun nemi gwamna Ganduje da ya sake wani zuwa na musamman kafian zafen zaben ranar asabar, saboda ganawa da kungiyoyi kwallon kafa da na wasannin daban daban da ke wannan katafariyar mazaba.
Gwamna Ganduje ya tabbatar masu da cewa zai kara komawa ranar Alhamis saboda a rabawa wadannan samari kayan wasanni na kulob kulob din su dake wannan mazaba da makwabtansu.
Dandazon al’ummar wannan yanki sunyi dafifi sun kara tabbatarwa da Gwamna Ganduje cewar suna tabbatar masa da kuri’unsu ba tare da wata matsala ba da taimakon Allah. Sun gaya masa kar ma ya yi wani dar kan maganar wannan zaben da za’a karasa. Gwamnan ya samu rakiyar Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas da Kwamishinoni da masu ba gwamna shawara da kuma dattawan Jam’iyya, kamar yadda kakakin fadara Gwamnatin Kano Abba Anwar ya shaidawa Jaridar Leadeship Ayau.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!