Connect with us

BIDIYO

Rasuwar Marigayi Rabiu Arrahuz Ta Girgiza Kannywood

Published

on

Rasuwar Marigayi Rabiu Arrahuz Ta Girgiza Kannywood

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

 

Rasuwar Alhaji Rabiu Arrahuz, wanda ya na daya daga cikin manyan fuodusoshi kuma ’yan kasuwa masu sayar da finafinan Hausa a masana’antar Kannywood, ta yi matuqar girgiza masu sana’ar shirin fim xin.

A ranar Juma’a 15 ga Maris, 2019 a ka wayi gari da rasuwar shahararren furodusan mai kamfanin Arrahuz Productions bayan fama jinya a asibitin qashi na Dala da ke birnin Kano sakamakon hatsarin motar da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa Gombe daga Yola.

Kaswancewarsa mai kyakkyawar alaqa da abokan sana’ar tasa su ka yi tururuwa su ka fita jana’izarsa, wacce a ka gudanar a Babbar Rana, wato Juma’a.

Kafin rawsuwar Alhaji Rabiu Arrahuz ya xauki nauyin shirya manya-manyan finafinan da su ka shiga tarihi a masana’antar kamar Risala, Macijiya da makamantansu.

A ’yan kwanakin nan marigayin ya xan ja baya da sana’ar fim tun bayan da hukumar tace finafinai na jihar Kano a qarqashin jagorancin Isma’il Afakallahu ta sa a ka kama shi; lamarin da a ke ganin shi ne sanadiyyar da ta sa Marigayi Arrahuz ya fara canja sana’a ya karkata ga fatauci a inda ya gamu da ajalinsa.

Abokan sana’arsa sun fi tunawa da shi Rabiu a matsayin mutum mai jajircewa da faxi-tashi wajen neman halak xinsa.

Ya rasu ya bar mata biyu da kuma ’ya’ya. Allah Ya gafarta ma sa, amin.
labarai

Share This

Share this post with your friends!