Connect with us

SIYASA

Wani Kusa A APC Ya Yi Tir Da Matakin INEC Na Ci Gaba Da Tattara Sakamakon Zabe A Bauchi

Published

on

Alhaji Salisu Barau wanda tsohon kwamishinan yada labarai ne a jihar Bauchi, kuma jigo a cikin jam’iyyar APC ya yi Allahwadai da matakin da INEC ta dauka na ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar daga karamar hukumar Tafawa Balewa a maimakon zuwa zagaye na biyu na gudanar da zaben.
Ya ce, matakin na INEC dai ya ci karo da umurnin da INEC din ta fara bayarwa a farko na cewar zaben gwamnan jihar ta Bauchin bai gama kammaluwa ba, inda ma ya ce INEC ta ajiye ranar 23 ga watan nan domin ci gaba da sake gudanar da zaben a wasu rumfunan zaben da aka samu cikas kamar a karamar hukumar Tafawa Balewa amma sai INEC din ta sake dawowa da cewar a ci gaba da tattara sakamakon zaben, ya ce hakan ya basu mamaki kana basu amince da matakin ba.
Da yake ganawa da ‘yan jaridu a Bauchi jiya, Salisu Barau ya shaida cewar shi daga karamar hukumar Tafawa Balewa yake, inda yake mai shaida cewar al’ummar karamar hukumar sun yi mamakin matakin INEC kana sun yi tir da shi, inda yake mai shaida cewar suna nan akan matsayar INEC na farko da ke cewar za a je zagayen zaben na biyu.
Ya ce, “Babu yadda za a yi INEC ta sanya jami’in da zai gudanar da aikin nan, ya kuma gudanar da aikinsa hadi da soke zaben karamar hukumar Tafawa Balewa, a bisa doka duk wanda bai yarda da wannan matakin ba sai dai ya je kotu, amma babu yadda za a yi a sake dawowa a sauya matsayar da jami’in zabe ya yanke wato Farfesa Kyari Muhammad jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi,” a cewar shi, INEC ce ta bashi aikin amma bai dace ya yi hukunci ta soke ba.
Ya kuma yi zargin cewar kwamitin gudanar da bincike kan soke zaben da INEC ta turo daga Abuja zuwa jihar ya ki sauraron bahasin jam’iyyar APC a lokacin da ke zaune da wakilan jam’iyyu inda ma ya yi zargin cewar ba a gayyacesu ba.
Barau ya ce, adalcin da INEC za ta yi shi ne ta amince da sake gudanar da zaben a karamar hukumar Tafawa Balewa domin fitar da hakikanin wnada ya smau nasarar lashe kujerar gwamnan jihar.
Da yake kuma gabatar da jawabi a lokacin da magoya bayan APC suka cika a ofishin jam’iyyar, Salisu Barau ya shaida cewar matsayar jam’iyyar APC dai shi ne a je gudanar da zaben a zango na biyu domin shine adalci ga kowa.
Wakilinmu dai ya shaida mana cewar dan takarar jam’iyyar PDP Bala Mohammed Abdulkadir dai yana saman dan takarar APC wanda shi ne gwamnan jihar a halin yanzu da kuri’u 4,059 a zaben da aka gudanar a kananan hukumomi 19 daga cikin 20 da suke fadin jihar.
A yau talata ne dai INEC za ta ci gaba da tattaro hadi da amsar sakamakon zaben gwamnan jihar daga karamar hukumar Tafawa Balewa, ana kuma sa ran INEC za ta sanar da sabon gwamnan jihar a yau din idan ta samu nasarar kammala tattara sakamakon zaben.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!