Connect with us

SIYASA

Zaben Cike-Gibi: A Guji Dan Takara Mai Dabi’ar Jaki, Kare Ko Kaza A Kano – Sheikh Khalil

Published

on

An bayyana cewa, tilas ne al’ummar jihar Kano su guji zaben duk wani dan takarar neman kujerar gwamnan Kano mai dabi’un jaki, kare da kaza a zaben cike gibi mai zuwa.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban Majalisar Malami ta Jihar Kano, Malam Ibrahim Khalil, a lokacin da LEADERSHIP A YAU ta yi ma sa tambaya kan wanda ya fi dacewa mutanen Kano su zaba a zaben cike gibi da za a gudanar na kujerar gwamna a jihar ranar Asabar 23 ga Maris, 2019.
Ya ce, “kullum mutane su rika fifita masalahar matasa da sauran al’umma wajen zaben shugaba jagora nagari ko da kuwa waye, idan dai ya na da jajircewa da hangen nesa da kuma burin sama wa al’umma kyakykyawar makoma ta ilimi da sana’o’i da ayyuka da mutuncinsu da darajarsu.
Malamin ya kara da cewa, “akwai bukatar a fifita abinda ya fi alkhairi, ba abinda ka fi so a ranka ko kuma abinda ka ke ki ba. Kowannenmu ya dauki masalahar cigaban al’umma ta fi tashi, kuma yin hakan shi ne hankali, shi ne nagarta mu guji ’yan siyasa masu dabi’ar karnuka, jakuna da kaza.
“Wannan shi ne zai fitar da mu gaci da samun kyakykyawar makoma a siyasa da shugabanci da zamantakewarmu da addininmu.”
Ya ce dabi’ar kare ita ce, rashin mutunci ta yadda duk wata nagarta kamar hakuri da juriya ta kare ya na da wata, illa wacce duk ta rusa wani abin yabo ga kare kamar yadda Turawa su ke yabon kare, domin idan ka dauke shi gadi, idan batagari sun zu su na kokarin samun ka duk haushin da ya ke yi idan ka jefa mi shi kashi ko kuli-kuli ko wani abu da ya ke so, to zai bar wannan haushin ya ci kayansa.
“To, akwai ’yan siyasa da duk rashin daidan abu, idan a ka jefa mu su wani abu da su ke so ko da wannan abin karya a ka yi mu su, sai ka ga sun yi ribas sun kuma kare karya da rashin mutunci. Dabi’ar kare kenan, ko guje su!
“Shi kuma jaki za ka ga sayen shi a ke yi da kudi, idan an saye shi an biya, to kaya a ke dora ma sa bai san kowane irin kaya ba ne; da kayan laifi da kayan litattafai duk bai sani ba. Shi dai an saye shi an biya, sai a yi ta dora ma sa kaya. Wannan shi ne dabi’ar jaki, ku guje shi!
“Sai dabi’ar kaza. Akwai ’yan siyasa masu dabi’ar kaza, wadanda su duk abinda ka ba su mai kyau sai sun je bola ko juji sun ci abinci, domin idan ka ba wa kaza tsabar gero ko dawa, to komai cin da ta yi sai ka gan ta a juji ta na cin datti da dai sauransu.
“Don haka mutane mu jajirce mu zabi shugaban da zai gina rayuwar al’umma, ba wanda zai zama koma-baya ba.”
Kasaitaccen malamin ya cigaba da cewa, “haka kuma wasu za ka ga su son zuciya shi ne a gabansu. Idan ka ba su kujerun Makka ko na Ummarah, to su a gurinsu ka gama yiwa addini hidima kuma ka zama mai kishin addini, wasu kuma a ba su kudi, ka zama nagari kenan, wasu kuma kwangila ko mukami. To, da yawa za ka ga nagarta a gurin wasu a kyautata mu su su kadai ba a kyautatawa al’umma ba kuma kyautatawa al’umma shi ne mafi alkairi, ba biyan bukatar kanka kawai ba.”
Sheikh Ibrahim Khalil, wanda ya bada misali ga tsaya wa tsayin-daka da daya daga cikin shehunan Musulunci su ka yi irinsu Shehu Ibrahim Inyass wanda ya yi na ishara da nuni a kan a zabi wani shugaba a zamaninsa, wanda da yawa ba a fahimce shi ba, sai bayan an yi zaben a ka ga alfanun abin, amma an yi ma sa maganganu da surutai masu yawa, amma da ya fifita masalahar al’umma bai damu da maganganun ba, sai abin ya zama alheri daga bisani.
“Haka shi ma Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi ya yi na tsaya wa tsayin-daka wajen wayar da kan al’umma a kan mahimmacin siyasa, amma ai ka ga ya sha kalubale, amman daga baya an ga amfanin masalahar yin hakan,” in ji shi.
Malam Khalil, ya nanata cewa, “haka kuma shi ma Ibn Taimiyya ya yi maganganu a kan ma’anar siyasa da masalahar al’umma, wanda har ma a ka yi maganar cewa Allah ya tsine wa wanda a ka ba shi kudi ya yi zabe a kan abinda ya saba wa masalaha da gaskiya.
“Haka kuma idan ka saurari wasu masana irinsu Lauya Bakarti Bulama da Dakta Dukawa a nan Kano ma sun bayyana cewa, duk da wannan zabe ba shi da wani muhalli, to amma tunda dai an ce za a yi shi, to ya na da mahimmanci mutane su fito su yi shi kuma su zabi shugaba wanda zai fifita masalaharsu a kan tasa da ba kuma ta ’yan kalilan mutane ba.
“A takaice dai bayanin masalahar al’umma shi ne ka yi tunani me ka rasa ka ke so ka samu, meye burinka, yaya za ka yi ka sama wa kanka mutunci da kasar ka da al’ummarka da duk dai wani abu da da ke nema ko ka rasa. To, a masalaha ka nemi yadda zai tabbata tunda na alkhairi ne. Kullum dai ka zabi abu mafi alkhairi ga al’ummarka ba a kashin kanka ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!