Connect with us

SIYASA

Halayen Dattaku Ne Suka Jawo Al’ummar Yobe Suka Zabi Mai Mala – Inji Alhaji Nuru

Published

on

An bayyana cewa halayen dattaku da sanin yakamata ne suka jawo al’ummar jihar Yobe yiwa Alhaji Mai Mala Buni ruwan kuri’un da suka bashi damar lashe zaben gwamnoni da yan majalisun dokoki da ya gabata a jihar; matsayin zababben gwamna mai jiran gado.
Wannan furucin ya fito ne daga bakin wani matashin dan siyasa a jihar Yobe, Nura Dalhatu Audu, a tattaunawar sa da wakilin mu a jihar- bayan kammala zaben, inda ya bayyana cewa suna kyautata zaton cewa Alhaji Mai Mala Buni wajen zai gudanar da mulkin jihar cikin adalci ga kowa.
“Wanda shaidar da muka yi masa ita ce, Alhaji Mai Mala, mutum ne mai gaskiya da rikon amana, an san shi da kwatanta adalci ga kowa. Mutum ne wanda jama’a suka yi masa shaidar kamun kai, kuma ba ya rike kowa a zuciya, sannan ba ya karbar gulma ko jita-jita”. Inji shi.
“Kuma bisa ga wadannan kyawawan halayen dattaku nashi, wadanda kowa ya yi masa shaidar su, muna da yakini kan cewa hakan zai taimaka masa wajen gudanar gwamnatin sa cikin tsanaki tare da aiki tukuru wajen ci gaban jama’ar wannan jihar. Saboda Hausawa sun ce: Laraba mai kyua tun daga Talata ake gane ta”.
Alhaji Nura ya sake bayyana cewa, sannan kuma idan ka hada da kwarewar da ya samu a mukamai daban-daban da ya rike, ya ce, a iya sanin da suka yiwa Alhaji Mai Mala Buni ba a taba Samun sa da wani tabon rashin gaskiya ko almundahana ba. “kuma duk ma’aikatar da ya zauna sai ta samu ci gaba da bunkasa- a rayuwar sa ya kafa tarihin samun nasarori bila adadin. Lamarin da ya jawo jama’a da dama ke tambayar miye sirrin tarihin wadannan nasarori wadanda Mai Mala ke samu”.
“Wanda yanzu haka ina rubuta littafi kan rayuwar Alhaji Mai Mala Buni, kuma ta wannan dalilin na ci karo da abubuwan mamaki dangane da rayuwar sa- wanda na takaita rubutun daga lokacin da ya rike shugaban jam’iyyar ACD, AC, babban mashawarci ga Gwamna Gaidam, kan lamurran siyasa da majalisar dokoki, shugaban jam’iyyar APC na farko a jihar Yobe, da rike babban sakataren APC na kasa”. Ya bayyana.
Bugu da kari kuma, ya bayyana babbar fatar da al’ummar jihar Yobe suke dashi dangane da gwamnatin Mai Buni da cewa, ko shakka babu, Gwamna Gaidam ya yi matukar kokari ta fuskacin bunkasa kowanne bangaren jihar Yobe- a shekaru 10 da ya yi a mulkin jihar, kuma wadanda ba zai yuwu mutum ya lissafa su ya dan karamin lokaci ba.
“haka zalika kuma, muna fatan zai ci gaba da kyawawan ayyukan bunkasa kowanne yankin jihar Yobe, kamar yadda gwamnatin da ya gada ta yi”.
“Bisa ga haka ne nake kira ga jama’ar Yobe kan su marawa wannan gwamnati mai zuwa ta Mai Mala, kamar yadda suka baiwa gwamnatin da ta gabata, ta Alhaji Ibrahim Gaidam. Kuma muna kyautata zaton hakan, idan an yi la’akari da ruwan kuri’un da al’ummar jihar Yobe suka bashi, a wannan zabe da ya gabata”. Inji Nura.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!