Connect with us

KASASHEN WAJE

Masu Nuna Kyama Ga Musulmi Sun Kai Hari A Masallatan Birtaniya Biyar

Published

on

Akalla masallatai biyar ne aka kaiwa hari a garin Birmingham na kasar Ingila, dukkan hare-haren an kai su ne da daren jiya, jami’an ‘yan sandan yankin Birmingham ne suka tabbatar da afkuwar lamarin da safiyar yau Alhamis.

Wadannan hare-haren sun biyo bayan wani hari da dan ta’adda ya kaiwa wasu masallata a yankin Christchurch na kasar New Zealand, inda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 50, tuni dai ‘yan sanda yankin Birmingham din sun fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan hare-haren.

Ana kara samun hare-haren ta’addanci daga masu nuna kyama ga musulmi a ‘yan kwanakin nan, musamman a kasashen yammacin turai, amma hukumomin tsaron kasar Ingila sun ce  ashirye suke wajen ganin sun dakile irin wadannan hare-haren.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!