Connect with us

RAHOTANNI

An Kashe Matashi Kan Rikicin Kungiyoyin Asiri A Lakwaja

Published

on

Wani matashi kuma magidanci mai suna Umar Faruk ya rasa ransa a hannun yan kungiyar asiri a lokacin da suka sassa reshi da muggan makamai, lamarin da tayi ajalinsa .
Wannan abin takaici dai ta faru ne a jiya laraba a yan kaji dake tsohuwar kasuwa dake birnin lakwaja a jihar Kogi. Umar Faruk, wanda akafi sani da suna Danladi Dealer, dan asalin unguwar tudun wada ne dake birnin zariya a jihar Kaduna. Lamarin ta faru ne da misalin karfe tara na safe a yayin da yan kungiyar asirin, wato Confoternity da Black Ades suka rika bata kashi da juna akan wani dalili wanda har lokacin hada wannan rehotu ba a san sanadiyar data janyo rikicin ba kuma da dama mambobin kungiyoyin asirin biyu sun samu munananan raunuka a lokacin bata kashin.
Wasu daga cikin yan kungiyoyin dai sun tsayar da Umar Faruk wanda yake sana,ar tukin A daidaita Sahu ko kuma Keke Napep ne, inda suka tilasta masa daya sauke fasinjojin da yake dauke dasu cikin A daidaita Sahun don ya kwashi mambobinsu da aka jiwa raunuka zuwa asabiti, amma kuma Umar Faruk yace sam hakan ba zata sabu ba. Daga nan yan kungiyar suka rika ja dashi i ala dole sai ya sauke fasinjojin daya dauko, lamarin data kai har sai data kai suka far masa da duka da sararsa da muggan makamai har @karfinsa inda suka barshi kwance jina jina, sannan suka ranta na kare . Daga bisani dai Umar faruk ya rasu kafin akai shi asibiti. Tunda farko rikicin kungiyoyin biyu ya faro ne tun daren talata a Unguwar Kabawa dake birnin na Lakwaja inda suka lalata ababen hawa irinsu motoci da Adaidaita Sahu da kuma babura kuma suka rika shiga gida gida sun dabawa mutane wuka.
Wakilin LEADERSHIP A YAU ASABAR wanda ya ziyarci Unguwar Kabawa ya tarad da jami’an tsaro a sassa dabam dabam na Unguwar domin tabbatar da doka da Oda tare da dakile duk wata barazanar tsaro daka iya tasowa a Unguwar. Jairidar LEADERSHIP A YAU ASABAR ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan jihar Kogi, Mista William Ayah domin jin ta bakinsa game da lamarin kuma ya tabbatarwa da Jaridar aukuwar lamarin inda yace rundunar ta kama mutane Uku da ake zargi, wadanda dukkansu suna dauke da raunuka a sassan jikinsu, sannan ya kara da cewa rundunar tana nan tana bincike kuma da zaran ta kammala binciken nata, zata gabatar da wadanda take zargin ga manema labarai.
Daga nan Mista William Ayah ya shawarci iyaye da su rika jawa yayansu kunne tare da kula da iren-iren mutanen da ‘ya’yansu suke mu’ammala da su domin kaucewa shiga kungiyoyin banza. Kakakin rundunan yan sandan a karshe yace rundunar ba za ta lamunci karya doka da Oda ba kuma shirye take tayi maganin duk wata haramtacciyar kungiya dake neman kawo barazanar tsaro a cikin al, umma.
A yan watannin nan dai, matsalar kungiyoyin asiri sun zama ruwan dare a birnin Lakwaja. Ko a kwanakin baya ma sai da wasu kungiyoyin na dabam suka yi arangama da juna a birnin na Lokoja inda da mutum biyu suka rasa rayukansu a yayin da dama suka samu raunuka kuma wannan lamari kamar yadda wani kwararre a fannin tsaro ,Aliyu Musa yace yana bukatar samun hadin kan gwamnati da iyaye da shugabannin addini dana al,umma da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro da kuma sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an shawo kan matsalar wanda a cewarsa yana neman zama annoba a cikin al, umma, inda kuma ya kara da cewa idan ba a dauki matakai ba, to hakan ba zai haifar da Da mai ido ba. Tuni dai akayi jana’izar Umar Faruk (Danladi Dealer )a birnin Lakwaja kamar yadda addinin musuluci ya tanada a ranar laraba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!