Connect with us

LABARAI

Hukumar Zabe Ta Tura Karin Kwamishinoni 3 Kano

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta tura karin Kwamishnonin zabe uku zuwa jihar Kano domin taimakawa wajen gudanar da zaben da ke guda a halin yanzu a jihar Kano na kammalawa. Kamar yadda aka sani Jihar Kano na cikin jihohi shida wadanda hukumar zaben ta bayyana sakamakon zaben Gwamnonin Jihohin da cewa ba su Kammala ba.
Kwamishinan Hukumar Zaben na Jihar Kano Farfesa Rakuwa Shehu ne ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da ya gudanar a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya ce an turo karin Kwamishinonin uku ne domin taimaka masa.
Wadanda aka turo din sun hada da Asma’u Maikudi daga Jihar Zamfara, Ganiyu Raji daga Jihar Ogun sai kuma Ahmad Mahmud daga Jihar Kebbi.
Farfesa Rakuwa Shehu ya ci gaba da cewa hukumarsa ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da zaben, ya kara da cewa rarraba muhimman kayayyakin zaben zai fara ne ranar Juma’a.
Shugaban Hukumar zaben na Jihar Kano ya bayyanawa jama’a kananan hukumomi, cibiyoyin zabe da kuma rumfunan zaben da ake gudanarwa a halin yanzu.
Raskuwa ya ce sake zaben zai shafi wasu kananan hukumomi guda 28 da suke da cibiyoyin rijsita 75 da kuma rumfunan zabe 207 wanda aka soke zabukansu, Jimlar masu kada kuri’ar da ake sa ran zasu halarci wannan zabe a dukkanin wuraren da aka ambata sun kai 128,324. Farfesa Raskuwa ya bayyana dalilan da suka sa aka soke sakamakon zabe a wadannan
wurare wanda ya ce hakan ta faru sakamakon hargitsi da kuma aringizon kuri’a.
Akwai kananan hukumomi 15 masu cibiyoyin zabe 116 wanda aka soke zabukansu sakamakon tashin hankali, yayin da kananan hukumomi 23 da suke da cibiyon kada kuri’a 91 aka soke sakamakonsu bisa dalilan aringizon kuri’a.
Farfesa Raskuwa ya ce zuwa yanzu Hukumarsa ta karbi Muhimman kayan zabe da sauransu kuma hukumar ta kammala raba wadannan kayan zabe a ranar, haka kuma Farfesa Raskuwa ya bukaci manema labarai su tabbatar da bayar da ingantaccen labarai kan zaben, sannan kuma ya bukace su da su kaucewa yada labaran da ba su da inganci domin kaucewa haifar da wata matsalar tashin hankula a Jihar Kano.
Hakazalika Raskuwa ya jadadda aniyarsa ta gudanar da sahihin zabe mai cike adalci, saboda haka sai ya bukaci al’umma da su zama masu kiyaye doka da oda a lokacin gudanar da zabukan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!