Connect with us

SIYASA

Jami’an Tsaro Sun Daidaita Akalar Zaben Cike Gurbi Na Kano

Published

on

Bayanan da ke fito wa daga jihar Kano sun nuna cewa, jami’an tsaro sun dauki matakan gaggawa wajen tabbatar da cewa komai ya tafi daidai a guraren da a ka kusan samun tangarda a yayin gudanar da zabukan cike gurbi na jihar da a ke gudanarwa a yau Asabar.

Tun da fari dai an samu rahotannin da ke nuni da cewa, a wasu daga cikin mazabun an so a samu hargitsi sakamakon zafin da bangarori biyu na manyan jam’iyyun jihar da ke fafatawa, APC da PDP, magoya bayansu su ka dauka.

An ruwaito rahotannin da ke nuni da cewa, jami’an tsaron sun kama kwamishinan ayyuka na musamman Muntari Ishak Yaksai, da dan majalisar dokoki na jiha Bappa Babba Dan’Agundi, amma daga bisani rundunar ‘yan sanda ta karyata hakan.

Bugu da kari, an samu hargitsi a wasu gurare na fashe-fashen kawuna. To, amma mafi yawan akwatinan zaben, an gudanar da komai lafiya ba tare da samun tashin-tashina ba.

Yanzu dai bayanai sun nuna cewa, komai ya lafa, bayan da jami’an tsaro su ka hana bangarori biyun tayar da kayar baya a rumfunan zaben da ake da matsaloli watakila saboda ganin alamun faduwa.

A tattaunawarsa da manema labarai, mukaddashin shugaban ‘yan sanda na kasa mai kula da zaben na Kano, DIG Antony Micheal Ogbizi, ya ce, “a Gama da ke karamar hukumar Nassarawa an samu fitowar jama’a sosai kuma zaben ya tafi lafiyar kalau.

“A ‘yan kalilan din wasu guraren inda a ka samu ‘yar tunja-tunja, mun shiga tsakani, don dawo da zaman lafiya.”

Ya kara da cewa, “ba su samu rahoton kawo ‘yan daba a zaben ba. Mu na da isassun ‘yan sanda. Jita-jitar cewa an kama wasu kwamishinoni karya ce tsagwaronta.”
labarai

Share This

Share this post with your friends!