Connect with us

LABARAI

Maimaita Zabe A Bauchi Yunkurin Durkusar Da Nasarar PDP Ne In ji Rhoda

Published

on

Hukumar zabe INEC ta ajiye ranar Asabar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta gudanar da zagayen zaben gwamnan jihar Bauchi zango na biyu.
Wata kungiyar siyasa mai suna, ‘Bauchi State Concerned Citizens’ ta yi zargin cewar tafiya gudanar da zagayen zaben gwamnan jihar Bauchi a zagaye na biyu a matsayin wani na yunkurin dakufar da nasarar dan takarar gwamna na PDP Bala Mohammed wanda yanzu haka shine ke kan gaba na samun rinjaye a zaben da aka fafata a ranar Asabar 9 ga watan Maris.
Kungiyar ta ce, jam’iyyar APC da INEC ne suke yunkurin kawo wa nasarar dan takarar jam’iyyar PDP nakasu wajen samun nasararsa.
Da take ganawa da ‘yan jarida a Bauchi jiya, shugaban kungiyar Misis Rhoda Jibrin ita ce ta yi zargin, tana mai karawa da cewa, INEC ta jefa al’ummar jihar cikin zullumi a sakamakon bayyana cewar sakamakon zaben gwamnan jihar bai kammalu ba.
Madam Rhoda ta shaida cewar hakkin INEC ne gudanar da zabe da fitar da wanda ya samu nasara, ta ce, ya saba wa doka babban kotun tarayya da ke Abuja ta tsaida ci gaba da tattara sakamakon zaben biyasa dogaro da korafin da gwamnan da ke ci a jihar Bauchi ya shigar a gabanta, ta ce shiga cikin lamarin da kotu ta yi ya saba wa dokar zabe, “bayan kammala aikin zabe ne duk wanda ke da korafi sai ya je kotu amma ba wai ana kan tattara sakamakon zaben kawai kotu ta dakatar ba,” Kamar yadda take cewa.
“A zahirin gaskiya babu wani da ke da ikon shiga cikin lamarin zabe a daidai lokacin da ake kan gudanar da aikin zaben. A fayyace yake, muddin aka fara gudanar da harkokin zabe, babu wani da ke da iko ko zarafin shiga cikin lamarin ko kawo radani a tattara sakamakon zaben ko bayyana wanda ya samu nasara. Dukkanin wani da ke da korafi akwai hanyoyi da matakan da aka gindaya bi bayan an bayyana sakamakon zaben,” A cewar ta.
Kungiyar Concerned Citizens ta bukaci hukumomin da abun ya shafa da su tabbatar da ayyana Sanata Bala Muhammad a matsayin wanda ya lashe kujerar gwamnan jihar Bauchi, “Ku gaggauta sanar da nasararsa cikin kankanin lokaci kawai domin kauce wa janyo tashin hankali a fadin jihar domin ci gaba da rike sakamakon zaben matsala ne sosai,” Inji Concerned Citizens.
Da take ba yani kan dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP, Misis Rhoda Jibrin ta ce dukkanin shaci fadin da wasu ke yadawa domin bata masa suna a matsayin yarfe ce kawai irin ta siyasa, “Kauran Bauchi ya yi wa mutane sosai ya kyautata wa jama’a fiye da yadda kuke tunani, ku bincika ko ku tambayi jama’an cikin Abuja ya suka ji dadinsa lokacin da yake Minista, ku tambayi al’umma a Bauchi yadda ya kyautata musu. Don haka zai daura ne kan halinsa na kyautata wa jama’an jihar Bauchi,” in ji ta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!