Connect with us

LABARAI

PDP Ta Yi Zargin Za A Kama Shugabanninta Na Jihar Bauci

Published

on

Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi zargin jam’iyyar APC mai mulki na kule-kulen cafke manyan jiga-jigan jam’iyyarta na jihar Bauchi, a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar PDP na kasa ya fitar, ya yi zargin ana kokarin kama jiga-jigan ne don a samu damar yin magudin zabe a zaben da ake sake gudanarwa a yau Asabar.

Sakataren jam’iyyar PDP din ya ce; rahotanni sun tabbatar musu jam’iyya mai mulki na kokarin amfani da ‘yan daba don tada hargitsi a rumfanan zabe, sannan suna zargin har an hada baki da wasu jami’an tsaro don a saci akwatinan zabe a wasu mazabun.

 

A biyo mu don samun cikakkun labarai…
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!