Connect with us

MANYAN LABARAI

Zaben Kano: Alamu Na Nuna Tarzoma Ba Za Ta Bar Zaben Ya Gudana Ba

Published

on

Alamu na nuna tashin hankula ba zasu bari a gudanar da sake zaben gwamna jihar Kano da ake gudanarwa a yau Asabar ba, zuwa yanzu an samu tashin hankula a wasu mazabu, misali a mazabar Beli ta karamar hukumar rogo har an soke zabe a wajen.

Masu kada kuri’a da dama sun ta rade-radin cewa ‘yan jagaliyar siyasa suna ta kaiwa mutane farmaki a rumfunan zabe daban-daban, sannan a mafiya yawan rumfunan zaben babu isassun jami’an tsaron da zasu masu kada kuri’a kariya.

Zuwa yanzu ba a fara kada kuri’a ba a wasu mazabun ma, a yayin da wasu kuma aka ce an fara kada kuri’a, amma ‘yan daba sun kori masu kada kuri’ar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!