Connect with us

RAHOTANNI

An Fara Kokawar Neman Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Published

on

Gabanin kaddamar da majalisar dattawa ta kasa a ranar 9 ga watan Yunin 2019, alamu na nuni da cewa, zawarawan kujerar shugaban majalisar dattawan ta kasa sun fada fadi-tashin ganin ta aure su.
Wannan zawarci a na yin sa ne ta hanyar neman hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki na siyasar kasar da kuma ita kanta majalisar.
Binciken LEADERSHIP A YAU LAHADI ya nuna cewa, wadanda ke gaba wajen neman kujerar sun hada da shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Ahmed Lawal da tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje da tsohon gwamnan jihar Nassarawa Sanata Abdullahi Adamu da tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar Sanata Ali Ndume.
Cikin wadanda a ke neman tubarrakinsu akwai jam’iyyar APC mai mulkin kasar, saboda kasancewar ita ce mafi rinjaye a majalisar. Sabanin a shekara ta 2015, a wannan karon rinjayenta ya fi yawa. Don haka ba a tsammanin jam’iyyar adawa ta PDP za ta samu mukamin mataimakin shugaban majalisar, kamar yadda ya faru a 2015 din.

A wancan karon bambancinsu bai wuce kujerun sanata guda goma ba, amma a wannan karon bambancin ya kusa hamsin. Don haka turjiya za ta yi sauki.
To, amma duk da haka a cikin ’yan mambobin majalisar dattawan guda 109 bakidaya, jam’iyyar PDP ta na kusan guda talatin, wanda hakan ke nuni da cewa, a cikin ’yan APC masu neman kujerar duk wanda ya fi samun tagomashin PDP zai iya yin tasiri.
Bugu da kari, daga dukkan alamu a wannan karon fadar shugaban kasa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta tsoma hannu don samar da shugaban majalisar da zai yi aiki tare da ita cikin sauki, sabanin yadda a 2015 ta nade hannu ta na kallo wanda ba nata ba ya zama shugaban majalisar, lamarin da ya sanya har a ka kawo karshen zangon mulkin gwamnatin na farko babu jituwa a tsakani, saboda yadda fadar shugaban kasar ta rika fuskantar cikas da fancale da majalisar wajen amincewa da wasu muhimman kudirce-kudircenta.
A cikin kudirorin da fadar shugaban kasa ta gaza cimma a karkashin majalisar ta ke kammala wa’adinta nan watan Yuni akwai kasa tabbatar da shugaban hukumar EFCC da kuma sabuwar dokar zabe, wacce majalisar ta rika kwan-gaba-kwan-baya a kanta.
A na danganta faruwar lamarin da sakacin fadar shugaban kasa a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari tun farko a lokacin da ya sake Bukola Saraki, wamda ba zabinsa ba ne ba kuma zabin jam’iyyarsa ta APC ba ne, ya zama shugaban majalisar tare da hadin gwiwar PDP.
Majalisar ita ce ta farko da a ka samu hatsin-bara ko gamin-gambiza wajen samar shugabancinta, inda shugaba da mataimakinsa su ka fito ba daga jam’iyya guda daya ba.
Daga dukkan alamu lallai a wannan karon fadar shugaban kasa da APC ba za ta su so irin hakan ta sake faruwa ba.
Baya ga fadar shugaban kasa, ita kanta PDP za ta so ya zamana ta na da hannu wajen samar da shugabancin majalisar ko da kuwa ba za ta ba ta mukami irin na baya ba, domin hakan zai bai wa ’ya’yanta samun shugabancin kwamitoci, baya ga shugaban marasa rinjaye, wanda da ma shi ne na marasa rinjayen a al’adance.
Akwai jigogin APC wadanda a ke ganin karfin fada-a-ji irin nasu ya kai a saka su cikin lissafin wadanda a ke neman dafawarsu, don samun wannan kujera ta shugabancin majalisar dattawa mai romo.
Irin wadannan mutane sun hada da jagoran APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Ahmed Bola Tinubu, wanda tabbas ya na da matukar tasiri a siyasar APC da ma kasar bakidaya.
Shi dai Tinubu a na ganin cewa, ko a 2015 bai ji dadin yadda Shugaba Buhari ya bar lamarin wasarairai har su Saraki su ka shammace su su ka samar da shugabancin ba tare da hannunsu ba, wanda hakan ya taba fada-a-jin Tinubu a siyasar kasar ta fuskar tasiri.
Su ma gwamnonin jihohi a yanzu a na ganin su na da tasiri wajen samar da sabon shugaban majalisar dattawan, domin su na da iko a kan yawancin sanatocin da a ka zabo daga jihohinsu.
Don haka wadannan masu neman shugabancin majalisar su na nan su na neman kamun kafa da su, don samun goya mu su baya, saboda su yi nasara, domin a al’adar siyasar kasar, gwamnoni su na iya juya akalar jam’iyya a jihohinsu, wacce ita ce ta ke bayar da tikitin da a ke tsaya wa takara da shi.
Bugu da kari, yanayin yadda yankunan siyasar su ke shi ma ya na tasiri wajen yakin neman zaben wannan kujera, domin ’yan takarar su na neman hadin kan ’yan uwansu sanatoci bisa la’akari da yankunan da su ka fito da kuma yankin da a ke maganar za a zabo shugaban majalisar dattawan daga cikinsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!