Connect with us

BUDADDIYAR WASIKA

Buhari: Lokacin Biyan Bashin Kanawa Ya Yi

Published

on

A matsayina na marubuci tsawon shekaru ashirin, banda addini na babu wani abu da na taba karewa da alkalamina tamkar Buhari. Tun dosowar zaben 2019, daga shekarar bara, a duk satin duniya Ina buga mukala wadda ke kare manufofin gwamnatinsa saboda na yarda cewa talakawa, musamman na arewa, sun yi amanar cewa Buhari mai kare musu hakki ne.
Tun a shekarar 2003, lokacin da Buhari ya fado tsundum cikin siyasa ya fara takarar shugaban kasa, Kanawa ba su taba yin kasa a gwiwa ba wajen yi masa ruwan kuri’u fiye da hatta jiharsa ta asali wato Katsina. A 2003, duk da hadarin fuskantar azabtarwa ta gwamnatin tarayya da iya rasa alfarma daga gare ta, Kanawa sun fito kwai da kwarkwata su ka kori gwamna mai ci, Rabiu Kwankwaso, da ke jam’iyya mai mulki su ka zabi Malam Shekarau. Haka Kanawa su ka yi ta ruwan kuri’u ga takarar Buhari a shekarun 2007, 2011, 2015 har zuwa wannan zabe na 2019.
Tun kafin zaben 2019 daidai lokacin da badakalar Ganduje ta bayyana, mutane irina da ke goyon bayan Buhari mun fito karara mun bada shawara cewa idan APC da Buhari su ka yi kuskuren gaza hukunta Ganduje ko da ta hanyar hana shi takara ne, a kwai hadarin APC zata fadi zabe a Kano.
Duk wanda ya san yadda siyasar Kano ke gudana tsawon shekaru ya san cewa talakawa za su kada Ganduje idan an zo zabe musamman ganin yadda a sama a ka ki cewa komai game da badakalarsa. Amma ’yan ba-ni-na-iya da ke Abuja su ka rufewa shugaba Buhari ido ya yarda a ka ba shi takara saboda a na su lissafin idan aka hana Ganduje takara Buhari ka iya rasa kuri’arsa ta Kano.
Duk wanda ya lura da Buhari ya san cewa baya son Ganduje saboda lamarin badakalar nan ta dala, domin a wajen taron kwamitin kamfen dinsa da aka kawo maganar zuwa Kano ya yi korafin cewa idan yazo Kano mai zai cewa talakawa idan su ka tambaye shi game da badakalar? Duk da haka iyayen jam’iyya da na kusa da shugaba Buhari sun sa ya zo ya daga hannun Ganduje. Shi kuma Ganduje ya na zaton cewa idan Buhari ya daga hannunsa fa shikenan ya ci zabe, saboda ya raina talakawa da ke jefa kuri’ar.
Masu tsare-tsare na APC sun kasa fahimtar cewa babu wani abu da zai raba Buhari da talakawan Kano idan dai ba Buharin ne ya canza akida ba. Don haka ko da Ganduje ko babu shi Buhari sai ya ci zabensa a Kano. Da sun bi shawarar tilastawa Ganduje yin murabus su ka canza shi da wani dan takara, da sun jefi tsuntsu biyu da dutse guda ta hanyar bawa APC nasara a Kano tare da tabbatar wa duniya, sabanin ikirarin yan adawa da ke cewa yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a kan yan adawa ya ke karewa.
Kuma ai ya kamata a ce Buhari ya wa’aztu da yadda Tinubu ya hana Ambode tsayawa takara a bisa laifin da bai kai rabin-rabin ta’asar Ganduje ba, kuma ga shi a yau Sanwa Olu ya ci zabe a Lagos.
A yau an saka Kanawa cikin dar-dar saboda sun fito sun yi hukunci kuma ana neman a murde musu. Kanawa sun yi watsi da gurbataccen shugabanci ya kamata a ji muryoyinsu. Abinda mutane ke kasa fahimta shine cewa wannan zabe ba fa tsakanin APC da PDP bane ko saboda Kwankwaso da Abba, a’a zabe ne tsakanin talaka da wadanda ya ke kallo a matsayin azzalumai. Laifin Ganduje ya wuce na karbar rashawar dala kawai a idon talakawa, musamman matasa. Kamar yadda na sha fada a baya, Ganduje dan jari hujja ne, kuma tsarinsa shine na kyautatawa manya (Attajirai, malaman gwamnati, sarakai da manyan ’yan boko).
Sannan a wanann lokaci nasa ya dawo da harkar dabar siyasa wadda shekarun mulkin Shekarau da na kwankwaso su ka yi kokarin dakilewa. Yawancin wadanda ke rike da madafen iko a gwamnatinsa mutane masu son kai wadanda kwakwalwarsu ba komai sai biyan bukatunsu. Ya yi watsi da harkokin ilimi gaba daya, matasa basa samun mafita a cikin tsare-tsarensa.
Tarbiya irin ta Fulani da malam bahaushe ta yi karanci a gwamnatinsa duk da ikirarinsa na Khadimul Islam. A tsakar daren jiya, mataimakinsa da babban kwamishina a gwamnatinsa, sun je karamar hukumar Nassaraw domin neman tada fitina kasancewarta wadda take ta karshe ta tabbatar da nasarar PDP. Kwamishina ya yi kokawa kamar dan jagaliya ko dan banga yadda saura kadan a yi masa tsirara. Shin irin wadannan mutane ne su ka cancanci mulkar mu a Kano?
Rokona ga Buhari da duk masu ruwa da tsaki shine su gaggaauta sanar da zaben a ba wanda ya ci kamar yadda a baya mu na gani yadda Bukola Saraki ya rungumi kaddara da shi da Akpabio, da Ajimobi, da Dankwambo kuma a ka hakura da nasarar da Dino Melaye ya samu da shi da Yakubu Dogara. Babu wani dalili da zai sa murde zaben Kano ko Bauchi. Wadanann garuruwa su ne yayan halak na Buhari kuma sun gaji da gwamnoninsu, don haka a ba su abinda su ka zaba.
Kokarin danne wadanna sakamako ba zai haifarwa siyasarmu da mai ido ba kuma idan wani yayi asarar ransa a dalilin haka hakika Baba Buhari ya ci amanar ’ya’yan halas dinsa da su ka tsaya tare dashi cikin ruwa da iska.
A karshe ina son duk wani dan APC musamman wadanda ke kan madafun iko a yau su tuna baya zuwa shekarar 2015. Shin yaya ransu zai kasance idan da Jonathan ya ki yi wa Buhari murna kuma ya ki yarda a fadi sakamakon zaben? Shin akwai wanda zai iya zama wani shugaba cikinsu?
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!