Connect with us

MANYAN LABARAI

Abubuwan Da Muke Sa Ran Buhari Zai Yi A Wannan Zangon – YCE

Published

on

Babban sakataren majalisar dattawan Yarabawa(YCE), ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da hadin kan al’ummar kasa.
Olajide ya bayyana kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa, lokaci ya yi da zai samar da hanyoyin da za su sa wannan kasar ta samu kudaden shiga, domin gudanar da wasu aikace-aikacen da za su bunkasa kasa.
NAN ya ruwaito cewa Olajide tsohon ma’aikacin lafiya ne kuma a halin yanzu yana rike da sarautar gargajiya.
“Na rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasikar taya murna da sake zabensa da aka yi, kuma na tabbatar masa cewa kungiyar YCE za ta ba shi cikakken goyon baya domin kai wa ga samun nasara.
“ A cikin wasikar da na rubuta masa, na nuna masa cewa, wannan nasarar da ya samu a karo na biyu nauyi ne ya karu a kansa, saboda haka ya tabbatar da cewa, ya yi amfani da wannan lokacin wajen hada kan al’ummar kasar nan, sannan kuma ya sake duba rahoton kwamitin El-Rufa’i kan sake wasu tsare-tsare.
“Shugaban kasa ya rubuto min amsar wannan wasika, inda ya nuna jin dadinsa tare da kara kawo wasu shawarwarinsa.
“Ya tabbatar min da cewa, dukkan shawarwarin da aka kawo za su duba domin yin aikin da su,” in ji shi.
Jagoran kungiyar Yarabawan ya ce, wannan kasa za ta samu ci gaba cikin gaggawa idan aka hada kan al’umma wajen gudanar da gwamnati yadda kowa zai bayar da ta sa gudummowarsa.
Sannan ya karfafa batun cewa ya kamata gwamnati ta sake duba kwamitin gwamna Nasir El-Rufa’i wanda shugaban kasa ya kafa a shekara ta 2017 kan sake duba shawarwarin da ya kawo.
“Ya kamata tunaninmu ya koma kan yadda za a samarwa kasar nan kudin shiga maimakon a dinga watanda da kudaden jama’a.
“Saboda ya kamata a ba kowane yanki damar bunkasa albarkatunsu.
“Kuma a samarwa wadannan wuraren cikakken tsaro cikin sauki, dukkan jami’an tsaro su bayar da gudummowarsu wajen bayar da kariya a irin wadannan wurare cikin sauki,” in ji shi.
Olajide jerin tsare-tsaren 14 a jamhuriya ta farko dukkan sauran tsre-tsaren na gwamnatocin jihohi ne.
Kamar yadda ya ce, yanzu akwai tsare-tsare guda 66 wadanda suka taimaka a lokacin mulkin sojoji a shekara ta 1966 suka aka samu gwamnatin hadin kai.
“Saboda haka, muna fatan nan da shekara hudu masu zuwa Buhari zai aiwatar da shawarwarin da kwamitin El-Rufa’i ya bayar.
“Ina ganin yana da matukar muhimmanci a fara aiwatar da shawarwarin wannan kwamitin domin tabbatar da gwamnatin hadin kan kasa.”
Sannan kuma ya yi kira ga shugaban kasa da babbar murya kan batun hadin kai, saboda haka sai ya roke shi da cewa ya tabbatar da cewa, kowane bangare na kasar nan an yi mata abin day a kamata, ta hanyar samar da ayyukan yi da kuma ayyukan raya kasa.
Ya kamata shugaban kasar ya yi amfani da damar daukar aiki da yin ayyukan raya kasa a lungu da sako na wannan kasa, domin bai wa al’ummar kowane yanki damar cin moriyar albarkar kasar nan kamar yadda tsarin mulki ya bayyana.
“Dole ne mu tabbatar da cewa, ci gaban Nijeriya ne a gabanmu ba nuna bambancin addini ko harshe ko yanki ba. Dole shugaban kasa ya tabbatar da cewa, an samu hadin kai a kasa.
“Haka kuma y ace ya kamata al’umma su bayar da ta su gudummowar wajen bunkasa kasa, musamman ma a bangaren tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”
Dangane da zaben da ya gudana kwanan nan kuwa, sai ya ce, an samu ci gaba a wannan kasa domin kuwa ya fi dukkan zabukan da aka yi a baya.
Olajide ya kuma bayyana ra’ayinsa na rage wa hukumar zabe ayyukan da take yi domin ta samu saukin gudanar da al’amuranta.
Ya ce ya kamata Hukumar zabe ta zama tana rijistar jam’iyyu kawai da kuma gudanar da zabuka. Sannan a kafa Hukumar da za ta Hukunta masu laifukan zabe.
Jagoran Yarabawan ya ci gaba da cewa, a tsame hannun sojoji daga kula da zabuka.
“Ina tattabar muku da cewa, na yaba da kokarin da shugaban Hukumar zabe ke yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!