Connect with us

SIYASA

An Shawarci Zababbun ‘Yan Siyasan Nijeriya

Published

on

An shawarci zababbu da suka sami nasara a zabubbukan da aka yi a wannan shekara tun daga na majalisun jiha da na tarayya ya zuwa shugaban kasa, da su tashi tsaye na ganin sun cika wa al’ummomin da suka zabe su alkawurran da suka yi ma su.
Wannan shi ne kawai zai sa al’ummar da suka zabe su, su yi murnar da zab en da suka yi ma su a madafun iko daban -= daban. Fitaccen Malamin nan da ke garin Kamfani a gundumar Duitsen – Abba da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna mai suna Shekh Malam Tanimuddari Mai Almajirai, ya bayar da shawar a zantawarsa da wakilinmu da ke Zariya, inda ya yi tsokaci kan nauyin da ke kan shugabanni da kuma wakilan da aka zaba a wannan shekara ta 2019 Shekh Malam Tanimuddari ya ci gaba da cewar, babu ko shakka babban abin da ke gaban zababbu ken an , yin ayyukan da za su tallafa wa al’umma ta bangarorin da suka hada da kiwon lafiya da ilimi da kuma bangarori da dama.
Game kuma da matsalolin tsaro, a cewar Shehin malamin da za a cewar, matsalar a kullun ta zama sanadin rasuwar mutane da dama, yayin da wasu kuma ke tsintar kan su a cikin ukuban rayuwa daban – daban.
Domin warware wannan matsala ta tsaro, Shekh Malam Tanimuddari Mai Almajirai, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma gwamnonin jihohi da su yi wushisshire – gyara zama ga matsalolin tsaro da addabar al’umma, musamman a jihar Zamfara da kuma wasu jihohi da suke arewacin Nijeriya.
Sauran hanyoyin da za su samar da zaman lafiya kamar yadda Malam ya ce, sun hada da yin adalci wajen yin shugabanci ko kuma wakilcin al’umma, sai kuma batun kyautatawa ga wadanda ake yi ma su mulki, abin nufi a cewarsa, in shugaban da aka zaba ko kuma wakilin da aka zaba ya tashi bayar da wani tallafi, sai ya cire son kai, wato, ya tsaya gab a da tallafi ko wani mukami ga wadanda suka zabe shi, in shugaba ko wakilin da aka zaba ya aiwatar da wannan tsari, bai adalci ba,domin daga lokacin da aka zabi shugaba ko wakili, ya zama shugaban kowa da kowa, haka shi ma wakili, in ya sami nasarar zabe ya zama wakilin kowa da kowa a mazabun da suke yi wa wakuilci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!