Connect with us

LABARAI

Bala Muhammad Ya Samu Nasarar Zama Gwamnan Jihar Bauchi

Published

on

A ranar Asabar ne aka gudanar da zagayen zaben gwamnan jihar Bauchi turmi na biyu. Da safiyar jiya Lahadi ne hukumar zabe INEC a jihar Bauchi ta amshi sakamakon zaben daga Turawan da suka tattara sakamakon zaben.
Zaben cike gurbin dai ya gudana ne a rumfuna guda 36 da suke cikin kananan hukumomin 15 a jihar ta Bauchi.
Farfesa Kyari Muhammad shine babban jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi, shine ya amshi sakamakon, inda babban Kwamishinan INEC da ke kula da jihohin Bauchi, Gombe da Yobe, Alhaji Baba Ardo da Kwamishinan INEC a jihar Bauchi, Ibrahim Abdullahi suka kasance a wajen amsar sakamakon zaben da aka yi jiya.
Wakilinmu ya shaida mana cewar dan takarar gwamnan Bauchi a jam’iyyar PDP Sanata Bala Muhammad ya sake samun nasara akan gwamnan jihar da kuri’u dubu 6,376 da ke neman sake zama a kujerar a karkashin jam’iyyar APC, Muhammad Abubakar mai kuri’un dubu 5,117 a zaben da aka sake gudanarwa a jihar.
Idan za ku iya tunawa Sanata Bala ya darar wa gwamna M.A a zaben farko da kuri’u dubu 4,059 ban da sakamakon zaben gwamnan jihar ta Bauchi a karamar hukumar Tafawa Balewa. Idan kuma kotu ta amince da zaben Tafawa Balewa Sanata Bala zai kasance yana da rinjaye a saman gwamnan da kuri’u 15,318.
Sakamakon zaben cike gurbin da aka amsa jiyan, APC ta samu kuri’u 5,117 a yayin da PDP ta samu kuri’u 6,376. Babbancin da ke tsakaninsu kuri’un dubu 1,259.
Sakamakon zaben Gwamnan Bauchi na farko dai APC tana da kuri’u 465, 453; ita kuma PDP tana da kuri’u dubu 469,512. Babbancin da ke tsakaninsu a zaben farko dai kuri’un 4,059. Idan aka hada da sakamakon zaben gwamnan jihar a Tafawa Balewa adadin nasarar PDP zai kara ninkuwa.
Dukkanin adadin kuri’un da suke a hukumance yanzu haka sune APC tana da kuri’u 470,570; PDP kuwa 475,888. Babbancin da ke tsakaninsu yanzu kuri’un dubu 5,318 jam’iyyar PDP ita ce ke kan gaba.
LEADERSHIP AYAU ta tattaro yadda sakamakon zaben ya kaya a kananan hukumomin 15 rumfuna guda 36 da aka sake zaben a cikinsu.
Karamar hukumar Bogoro: APC 101 PDP 478; Karamar hukumar Misau: PDP 312, ita kuma APC ta samu kuri’u 111; Karamar hukumar Dass PDP 358, APC 184; Karamar hukumar Darazo: PDP 749, APC 824; Karamar hukumar Shira PDP 86, APC 152; Karamar hukumar Ningi: PDP 791, APC 758; Karamar hukumar Ganjuwa: PDP 353, APC kuma 432; Karamar hukumar Gamawa: PDP 95, APC 154.
Sauran kananan hukumomin da aka sake zaben a cikinsu sun hada da Karamar hukumar Kirfi: PDP ta samu kuri’u 473 a yayin da APC ta samu 206; Karamar hukumar Shira: PDP 86, APC 152; Karamar hukumar Itas Itas Gadau; PDP 619, ita APC kuma 421; Karamar hukumar Alkaleri: PDP 444, APC 264; Karamar hukumar Toro: PDP 828, APC 536. An samu matsalar da ta haifar da soke zaben rumfar Tamar 498 a sakamakon dangwala kuri’un fiye da kima. Sai kuma karamar hukumar Katagum. PDP 203, APC ta samu 261, An soke zaben rumfar Madagala 03 mai adadin masu rijista 989 a sakamakon dangwala kuri’ar fiye da kima; sai kuma karamar hukuma ta karshe wanda PDP ta samu 57, ita kuma APC ta sami 74, An soke zaben Jama’are E , rumfa ta Kagori a sakamakon tayar da hankali da aka yi a lokacin zaben, rumfunar na da masu zabe 524.
Sanata Bala Muhammad na jiran sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi a karamar hukumar Tafawa Balewa ne kawai ya zama sabon gwamnan jihar Bauchi. Bincikenmu ya gano mana cewar koda kotu ta amince da sakamakon zaben gwamnan jihar a karamar hukumar Tafawa Balewa Sanata Bala ne ke da rinjaye, idan ma ta yi watsi da sakamakon zaben a karamar hukumar kawo yanzu shi Sanata Bala shi ne ke kan gaba.
INEC ta ce, sakamakon zaben a karamar hukumar guda daya ne kawai yanzu ya rage musu, hakan kuma ya faru ne a sakamakon shigar da kara da gwamnan jihar Muhammad Abubakar ya kai yana kalubalantar zaben gwamnan jihar a karamar hukumar Tafawa Balewa. Yau ne dai ake sa ran kotun za ta yanke hukunci na karshe kan wannan babin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!