Connect with us

WASANNI

Ban Kulla Yarjejeniya Da Real Madrid Ba

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard, ya bayyana cewa har yanzu bai kulla wata yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ba kamar yadda rahotanni suke ruwaitowa.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta dade tana zawarcin dan wasa Hazard wanda kungiyar take fatan zai maye mata gurbin tsohon dan wasanta Cristiano Ronaldo wanda yakoma Jubentus.
Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa Hazard ya kulla yarjejeniyar shekara biyar ad Real Madrid domin bugawa kungiyar wasa a kakar wasa mai zuwa sai dai dan wasan ya karyata zancen inda yace labarin ba gaskiya bane.
“Bani da wata yarjejeniya da Real Madrid a halin yanzu saboda haka yanzu hankalina yana kan wasan da kasarmu ta Belgium za ta buga da kasar Cyprus a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar turai”
Yaci gaba da cewa “Yanzu ba lokacin magana bane akan sauya kungiya saboda kakar wasa tazo karshe kowacce kungiya da ‘yan wasanta yanzu sun dukufa wajen ganin sun kammala kakar wasa cikin nasara”
Wasu rahotanni dai daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi wa Hazard farashin kudi fam miliyan 89 wanda hakan ake ganin babu kungiyar da za ta iya biyan kudin sai Real Madrid.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!