Connect with us

Da dimi-diminsa

Ban Taya Sanata Bala Murnar Lashe Zabe Ba, Inji Gwamnan Bauchi

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar ya karyata wani rubutun da aka yada a kafafen sadarwar zamani da ke cewa ya tura sakon taya murna ga Sanata Bala Muhammad a matsayin sabon gwamnan jihar Bauchi.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru daga sakataren gwamnan jihar Bauchi, Abubakar Al-Sadique da ya aiko mana, ya ce batun da aka yada a kafafen sadarwar zamani karyace kawai aka shirya, yana mai shaida cewar suna da hanyoyin da suka dace na aike da takardar manema labaru ga ‘yan jaridu wanda a cewarsa ba su tura wani batu makamancin wanda ake yadawa ba.

Don haka ne ya nemi jama’a da su yi watsi da wancan batun.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!