Connect with us

WASANNI

Barcelona Za Ta Bayar Da Malcom Domin Daukar Hudson Udoi

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fara shirin tuntubar kungiyar Chelsea a kan dan wasa Hudson Udoi domin ta bayar da sabon dan wasanta data siya daga Bourdeud domin ta dauki dan wasan dan kasar Ingila.
Zakarun na kasar Sipaniya dai sun nemi dan wasa Willian a kwanakin baya inda suka taya dan wasan har sau biyu amma kungiyar Chelsea tace dan wasan nata bana siyarwa bane hakan yasa kungiyar ta hakura sai dai yanzu kuma suna zawarcin matashin dan wasa Udoi Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dai ta dage cewa dan wasan nata bana siyarwa bane hakan yasa shima dan wasan wanda da farko ya nuna cewa yanason tafiya ya hakura da tafiya bayan kungiyar ta tabbatar masa da cewa bazata siyar dashi ba.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ce ta nemi dan wasan a watan Janairun daya gabata inda har ta taya dan wasan akan kudi fam miliyan 50 sai dai Chelsea ta bayyana cewa ba za ta yarda ta rabu da matashin dan wasan ba
Malcon wanda koma Barcelona akan kudi fam miliyan 35 daga kungiyar kwallon kafa ta Bourdeuad ya ka sa nuna kansa a kungiyar ta Barcelona inda ya buga wasanni biya kacal a kungiyar.
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta shirya yin asara a kan Malcon kuma za ta bayar da dan wasan sannan ta cika wa Chelsea kudi ta karbi Hudson Udoi wanda shi ma matashin dan wasa ne kuma a wannan satin ya bugawa kasar Ingila wasa. Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara neman dan wasa Udoi sai dai abune mai wahala Chelsea ta siyar mata da dan wasan wanda take ganin nan gaba zai zama babban dan wasa a duniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!