Connect with us

WASANNI

Bazan Bar Real Madrid Ba, Cewar Barane

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Rafael Barane, ya bayyana cewa babu gaskiya a labarin da ake yadawa cewa yana shirin barin kungiyar domin sake sabuwar kungiya da kuma sabuwar gasa kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana cewa ya gayawa Real Madrid cewa yana son su bashi dama yatafi.
Wasu jaridu a kasar Sipaniya ne suka bayyana cewa tuni dan wasan ya bayyana cewa y agama shirin barin Real Madrid kuma har ya gayawa shugaban kungiyar burinsa na sake sabuwar kungiya.
Sai dai Barane ya tabbatar da cewa bashi da burin barin Real Madrid kuma duk wanda yake yada jita jitar cewa zai bar Real Madrid bakaryaci ne kuma bai san aikinsa saboda yana farin ciki a kungiyarsa.
Barane dai yana buga kakar wasa ta takwas a Real Madrid bayan ya koma kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Lens dake kasar Faransa a lokacin da Jose Mourinho yake koyar da kungiyar ta Madrid wadda yashafe shekaru uku.
Kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan akan kudi fam miliyan 87 domin yakoma kasar Faransa da buga wasa a kakar wasa mai zuwa. s
Barane ya koma Real Madrid ne yana dan shekara 18 kuma ya lashe kofin zakarun turai sau hudu sannan kuma yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan baya da duniya take ji dasu yanzu wanda hakanne yasa manyan kungiyoyi suke zawarcinsa.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ma tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan bayan da tun a kakar wasan data gabata kungiyar ta taya dan wasan amma Real Madrid tace bana siyarwa bane.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!