Connect with us

WASANNI

Dole Sai Mun Sake Dagewa, Cewar Kociyan Nijeriya

Published

on

Kociyan tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya, Gernot Rohr, ya bayyana cewa duk da cewa sun samu nasara a wasan da suka doke kasar Sychelles daci 3-1 a wasan karshe na neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa amma har yanzu akwai bukatar sake dagewa daga ‘yan wasa.
Samun nasarar da Najeriya tayi yasa yanzu tasamu tikitin zuwa gasar cin kofin nahiyar Africa da wanda kasar Masar wato Egypt zata karbi bakunci a watan Yuni na shekara mai zuwa bayan ta buga wasanni shida kuma tasamu maki 13.
Rohr ya ce duk da cewa sun samu nasara amma kuma kasar Sychelles sun bawa tawagar ‘yan wasan wahala sosai kuma yana kira ga ‘yan wasan tawagar dasu sake shiryawa domin tunkarar gasar ta Africa.
“Munci kwallon farko ta hanyar bugun fanareti sannan kuma munyi kura kurai wanda hakan yana faruwa ga kowacce kungiyar amma daga baya kuma mun sake samun kwallaye biyu wanda abin farin ciki ne.
Najeriya ce ta ja ragamar rukuni na biyar da maki 13, sai Afirka ta Kudu wadda ta yi wasa biyar da maki tara har ila yau Najeriya ta yi nasarar cin kasar Seychelles 3-0 a wasan farko da suka fafata ranar 8 ga watan Satumba.
Kasar Libya wadda ita ma ta yi karawa biyar tana da maki bakwai a mataki na uku, sai Seychelles ta hudu mai maki daya kacal bayan karawa shida da ta yi kuma itace kasar da take da karancin maki a wasannin neman cancantar gaba daya a nahiyar Africa.
Kasar Masar ce za ta karbi bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka da za a fara ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuni sai dai da farko kasar Kamaru aka bawa damar daukar nauyin gasar amma daga baya hukumar kwallon Africa ta CAF ta kwace saboda rashin cikakken shiri.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!