Connect with us

SIYASA

El-Rufai Da Uba Sani Alheri Ne Ga Al’ummar Kaduna – Inji MS Ustaz

Published

on

An bayyana sake zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, a matsayin wani gagarumin nasara ga daukacin Al’ummar Jihar Kaduna da ma Nijeriya ba ki daya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani babban jigo a jam’iyyar APC, wanda kuma shi ne Darakta mai kula da ayyuka na musamman na APC dake tsakiyar Kaduna, a yayin zaben wannan shekarar ta 2019, Honarabul Muhammad Sani Abdul-Majid, wanda aka fi sa ni da MS Ustaz, a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake kaduna.
MS Ustaz ya ci gaba da cewa, “Muna godiya ga Allah(SWA), da ya bamu ikon sake zabar wadannan bayin Allah domin su ci gaba da ayyukan alkhairi da suka dauko yima Al’ummar Jihar kaduna da kuma kasa baki daya.”
“Tabbas Al’ummar Jihar kaduna sun yi dace da jajirtaccen kuma hazikin gwamna, domin a bayyana ne yake babu wani gwamna da ya kai Gwamnan kaduna zuba ayyuka ga jama’ar jiharsa. Wannan na cikin dalilin da wasu ke masa lakabi da magajin Baba Buhari, idan Allah ya kaimu shekara ta 2023 mai zuwa.”
Honarabul MS Ustaz, ya kuma mika godiyarsa na musamman ga daukacin Al’ummar Jihar kaduna, musamman Al’ummar kaduna ta tsakiya, bisa yadda suka jajirce wajen ganin sun zabi Malam Uba Sani, a matsayin zababben Sanatan Kaduna ta tsakiya a inuwar jam’iyyar APC. A cewarsa, yana da yakinin cewa, Insha Allahu, Malam Uba Sani, ba zai basu kunya ba.
Da kuma yake amsa tambayoyi akan irin jita jitan da wasu ke yadawa na rasuwar Gwamnan Jihar kaduna? MS Ustaz ya ce,” Manzon Allah (SAW) ya ce, duk Shugaban da yazo da alheri, dole a samu masu yi masa shairi da kage a kansa. domin haka, wannan ba abun mamaki ba ne, ga irin wannan mutane. Amma ina kira a garesu da su sani cewa, ta Allah ba tasu ba, domin Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana Mazuru Ana Shaho sai ya yi.”
Da kuma yake amsa tambaya Akan kiraye kirayen da wasu Al’ummar ke yi, na ganin Gwamnan Jihar kaduna, ya sanya sunansa a cikin jerin sunayen Mutanen masu himma da kwazo da zai baiwa mukamai a jerin sababbin nade naden da zai gudanar a cikin zagayen gwamnatinsa karo na biyu? Honarabul Muhammad Sani Abdul-Majid cewa ya yi, “ Babu abin da zance ga Al’ummar da kullum suke yi mana fatan alheri, fa ce Allah ya zaba mana abin da shi ne yafi alheri a garemu, da jiharmu baki daya, domin mu burinmu a kullum bai wuce na kyautata ma Al’umma, da sadaukar da kanmu a garesu ba.”
Daga karshe ya yi kira ga Shugaban kasa Muhamadu Buhari da Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru El-rufai, da cewa, suyi kokarin zabo mutane masu amana da kishin kasa wajen basu mukamai, ba mutanen da kansu da aljihun kawai suka sani ba. A cewar, MS Ustaz
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!