Connect with us

MANYAN LABARAI

Ganduje, Tambuwal, Kauran Bauchi Sun Lashe Zabe Da Kyar

Published

on

  • Lalong Da Ortom Sun Lashe Jihohins

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu nasarar lashe zabe a kamala zabe da aka yi da kuri’a 45,876.
Jami’in tattara sakamakon zaben jihar Farfesa B. B Shehune yabayyana wannan sakamakon zaben wanda ya ce, “ Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ne ya samu nasarar lashe zaben da kuri’a 45,876 ya yin da abokin takararsa na jama’iyyar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’a 10,239.
Farfesa Shehu ya ce an gudanar da zaben a kananan hukumomi 28, wanda suke da yawan masa kuri’a 131,073.
Sai gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal na jam’iyyar PDP wanda shi ma jami’ar tattara sakamakon zabe ta jihar, shugabar jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse Farfesa Fatima Muktar ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasa a kan abokin takararsa Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a zaben da ya gudana. Gwamnan ya samu nasarar doke abokin karawar ta sa ne da kuri’a 512,002 yayin da APC ke da 511,661.
Sai gwamnan jihar Filato Simon Lalong, na jam’iyyar, APC, jami’in tattara sakamakon zaben jihar ta Filato Farfesa Richard Kimbir ya bayyana cewa, ya samu nasara da kuri’a 595,582 a kan abokan takararsa wanda ya kayar da abokin hamayyar ta sa na jam’iyyar PDP mai kuri’a 546,813.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!