Connect with us

MANYAN LABARAI

Gwamnatin Tarayya Ta Biya Naira Biliyan 201 Ga Wadanda Suka Yi Ritaya A 2017 — Pencom

Published

on

Tsakanin watan Afrailun shekarar 2017 da kuma watan Junairun wannan shekarar, gwamnatin tarayya ta saka naira biliyan 201.95, a asusun hukumar fansho wacce take karkashin kulawar babban bankin Nijerya. Wannan kudade ne wadanda aka tattara na ma’aikatan gwamnatin tarayya kafin a bayyana saban tsarin na shekarar 2004. Gwamnatin tarayya tana ware kudadan a kasafin kudin duk shekara.
An sami wannan alkaluma ne daga hukumar fansho ta kasa wanda yake nuna dukkan kudaden da aka ijiye a asusun ma’aikatan fanshon gwamnatin tarayya tun daga watan Afrilun shekarar 2017 har zuwa watan Junairun shekarar 2019, wanda ya kai na naira biliyan 205.16.
Wannan alkaluma yana kunshe ne a takardar da mukaddashin shugaban hukumar PenCom, Aisha Dahir-Umar, ta tura wa kwamitin majalisar wakilan musu kula da harkokin binciken hukuumar. A cikin takardar, hukumar ta bayyana kudadan da aka ijiye na ma’aikatan fanshon wanda take kula da su.
An karanta kamar haka, “Duka kudaden da gwamnatin tarayya ta biya a cikin asusun tsofaffin ma’aikata wanda babban bankin Nijeriya take kulawa tun daga watan Afrailun shekarar 2017 har zuwa watan Junairun shekarar 2019, sun kai naira 201, 958, 183, 018.00
“Hukumar ta yi amfani ne da asusun bai-daya na babban bankin Nijeriya, inda ba ta yi amfani da wata asusun a banki masu zaman kansu ba. “Ina da muhimmanci a san da cewa, shi kudaden ma’aikatan fanshon ana tattara su ne tun daga ofishin akawun gwamnatin tarayya, sannan a zuba su a asusun ‘yan fansho musamma ma wadanda suke biyan kudi na tsarin albashi na IPPIS.
“A bangare daya kuma, ma’aikatan fansho wadanda ba a biyan su albashi ta tsarin IPPIS, ana biyan su ne daga ofishin akawun gwamnatin tarayya wanda babban bankin Nijeriya ke kula da shi har zuwa asusun ma’aikata.”
A takardar, hukumar ta bayyana cewa, dukkan kudaden kaddarorin fanshon ya karu da naira tiriliyan 8.63 a watan Disambar shekarar 2018, tare da saka naira biliyan 29.15 duk wata. Ta ce, dukkan kaddarorin fanshon daidaita da kashi 7.40 na jimillan kudaden da suke shigowa kasa.
Takardar ta nuna cewa, a watan Disambar shekarar 2018, mutum 260,808, sun yi ritaya daga aiki. A cewar hukumar PenCom, wadannan mutum 260,808 wadanda suka yi ritaya, suna amsar kudin fanshonsu na naira biliyan 10.18 duk wata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!