Connect with us

MANYAN LABARAI

INEC Ta Tabbatar Da Harbin Jami’ar Zabe A Jihar Benuwai

Published

on

Kwamishiniyar hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Benuwe, Dakta Nentawe Yilwatda, ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka kaiwa tawagar hukumar zaben a kan hanyar Gboko zuwa Makurdi, a ranar Asabar da dare.
Yilwatda, ta shaidawa manema labarai hakan a safiyar ranar Lahadi, a shalkwatar hukumar zaben da ke Makurdi, inda ta ce, harsashi ya sami babbar jami’ar zaben na Gboko, Farfesa Comfort Tuleun, a lokacin da aka kaiwa tawagar harin.
“Da gaske ne, wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko su waye ba, sun kaiwa tawagar hukumar zaben wadanda suke komowa daga karamar hukumar Gboko zuwa nan Makurdi, hari ne a ranar Asabar, da misalin karfe 8 na yammaci, bayan sun kammala zaben gwamna da na ‘yan majalisun Jiha.
“A lokacin harin, wanda a cikin tawagar akwai ma’aikatan hukumar zaben, jami’an tsaro na karamar hukumar Tarka, babbar jami’ar tattara sakamakon zaben, Farfesa Comfort Tuleun, wacce harsashin ya same ta, a yanzun haka tana karban magani a Asibiti.
“Ita babbar jami’ar tattara sakamakon zaben ta zo ne daga jami’ar koyar da ayyukan gona ta tarayya da ke Makurdi.
“INEC ta yi jimamin faruwan hakan, ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su dukufa na ganin sun kama batagarin da suka aikata hakan domin gurfanar da su a gaban shari’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!