Connect with us

SIYASA

Kayan Haihuwa Na Naira Miliyon 150 Gwamnatin Kano Ta Rabawa Mata

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta raba Jakar kayan Haihuwa 10,000 ga mata masu ciki a Jihar Kano wanda jimlar kudin su ya kai Naira Miliyon 150.
Shirin raba jakar kayan Haihuwar wanda ya kunshi Kananan Hukumomin Jihar Kano 15 wanda kowace jaka ta kunshi abubuwan da mai haihuwa ke bukata.
Gwamnan Kano Dakta AbdullahiUmar Ganduje wanda mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya wakilta ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin raba kayan haihuwar kyauta ga mata 2,000 wanda aka gudanar a cibiyar lafiya dake Unguwar Gama cikin Karamar Hukumar Nasarawa.
Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya ci gaba da cewa wannan Gwamnati na baiwa harkokin lafiya kulawa ta musamman shirin harkar lafiya kyauta ga mata masu dauke ciki a Jihar Kano, Ya ce, shirin na yau ci gaba ne na raba wannan jakakkunan kayan haihuwa wanda mata 2,000 za su amfana, wadda kowacce mace za ta yi hafzi jaka guda daga cikin wadannan jakakkuna dake kunshe da kayan da mata masu ciki ke bukata a lokacin haihuwa da kuma bayan haihuwar.
Gawuna ya ci gaba da cewar, wannan gwamnati ta shirya gudanar wannan shiri horarwa na watanni 18 ga unguwar zoma wanda bayan kammala samun horon kuma za’a tura su karkara domin tallafawa hakokin haihuwa. A cewar Mataimakin Gwamna sama da mata unguwar don 1,936 aka baiwa horo na musamman kan yadda zasu iya fuskantar matsalolin haihuwa, ya kara da cewa Gwamnatin Kano ta samar da Babura masu kafa uku wanda za a yi amfani da su wajen daukar mata masu ciki zuwa asibitoci daban daban.
Hakazalika Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa aikin idon da aka kammala a asibiiti Isa Kaita inda sama mutane 150 suka amfana, ko shakka babu an samu gagarumar nasara, inda ya nuna cewa daga cikin mutane 3,000 da suke da matsalar ido sun samu maganunuwa da kuma tabarau kyauta. Don haka sai ya tabbatarwa da al’umma cewar wannan Gwamnati za ta ci gaba da samar da ingantattun ayyukan ci gaba domin inganta lafiyar al’ummar Jihar Kano.
Tunda farko ana sa jawabin Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya na Jiha Kano Dakta Kabir Ibrahim Getso cewa ya yi a kokarin Gwamnatin Kano na inganta harkokin lafiya, Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta gyara asibitoci masu yawa a fadi Jihar Kano.
Dakta Kabir Ibrahim Getso ya ci gaba da cewa bayan wadannan ayyuka kuma Gwamnatin JIhar Kani ta dauki ma’aikatan Lafiya domin cike gibin da ake dashi na ma’aikatan lafiya domin inganta harkokin lafiya.
Saboda haka sai kwamishinan ya bukaci wadanda suka amfana da wannan tagomashi da su yi kyakkyawan amafani da kayan da suka samu tare da saka kyauta da hukunci ta hanyar fitowa gwansu da kwarkwata wajen sake zabar Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje a zaben da sake ranar 23 ga wata Maris na shekara ta 2019. Kamar yadda mai magana da yawun Mataimakin Gwamnan Kano Hassan Musa Fagge ya shaidawa Jaridar Leadership A Yau.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!