Connect with us

MANYAN LABARAI

Nijeriya Na Cikin Hadari Fiye Da Kowanne Lokaci – Obasanjo

Published

on

Tsohon shugaban kasan nan, Olusegun Obasanjo, ya koka a kan matakin da rashin hadin kai ya kai a kasar nan, ya karfafa cewa, lamarin rashin hadin kan a halin yanzun ya zarta na lokacin yakin basasan kasar nan.
“In muka yi dubi a kasar nan a halin yanzun, ko a zamanin yakin basasan, rabuwar kan namu bai kai na yanzun ba. muna cikin mummunan hadari ne a yau, matukar ba mu karfafa zumunta a tsakaninmu ba,” in ji shi.
Obasanjo ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, lokacin taron shekara wanda kungiyar manyan masu binciken kudi na bankuna suka shirya, wanda aka yi a Abeokuta, ta Jihar Ogun.
Obasanjo ya kuma yi kira ga shugabanni da su dauki lamarin gudanar da aikin gwamnati da mahimmanci, musamman in an yi la’akari da yanda yawan al’umman kasar na ke ta karuwa.
Ya yi imani da cewa, in har gwamnati ta san abin da take yi, nan take za a iya kawar da jahici daga al’umman kasa, wanda hakan zai iya samar da ci gaban al’umman.
Tsohon shugaban kasan ya yi kira ga shugabanni da su samar da ingantaccen Ilimi ga al’umman kasa, gidaje, ayyukan lafiya, musamman ma samarwa da al’umman ayyukan yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!