Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Na Samar Da Tan Miliyan 55.85 Na Ma’adanai –NBS

Published

on

A bisa bayanan da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar a ranar Alhamis data gabata ta bayyana cewar, Nijeriya ta samar da tan miliyan 55.85 na ma’anai a cikin shekarar 2018.
Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin rahoton da hukumar ta fitar, inda ta kara da cewa jihar Ogun it ace akan gaba wajen ma’anai daga cikin jihohi 36 harda babban birnin tarayyara Abuja.
Rahoton ya kara da cewa, jihar Ogun tana samar da ma’adanai da suka kai tan miliyan 16.49, inda rahoton ya yi nuni da cewa, hakan ya kai kashi 30 bisa dari na jimalar tan na ma’adanan da aka samu a cikin shekarar.
hukumar ta bayyana cewar, jihohi Kogi da Koros Ribas sune suke bi mata a baya a inda suke samar da ma’adanain da yawan su ya kai tan miliyan 15.13 da kuma tan miliayn 3.49, inda hakan ya kai yawan kimaninkashi 27 da kuma kashi shida na jimar ma’adana da aka samar.
Har ila yau, a daya bangaren kuma, rahoton ya bayyana cewar, jihohin Bayelsa da Borno suna samar da ma’adanai da yawan su ya kai daga sifili zuwa tan 8,403.30.
Acewar rahoton ma’adanan da aka samar a shekarar 2018 sun nuna cewar, Nijeriya ta samar da ma’adanai tan miliyan 55,850,075.43, inda jihar Ogun ta samar da mafi yawa daga cikin jihohi 36 harda Abuja.
Jihar ta samar da ma’adanan da yawan su ya kai tan 16,497,405.35, indahakan ya kai kashi 30 bisa dari na wanda aka samu a cikin shekarar.
Acewar rahoton duwatsun alfarma na (limestone) suna samar da ma’adanai da yawan su kai tan miliyan 27.19 a shekarar 2018, inda hakan ya kai kimanin kashi 49 na yawan ma’adananan da aka samar.
A karshe rahoton na hukumar NBS ya ce, dutsen Granite da dutsen Laterite, inda yake bi msa da tan miliyan 9.62 da kuma tan miliyan 5.07 da aka sama, inda hakan ya kai kashi 17 da kashi 9 na jimlar tan na ma’adanan a shekarar ta 2018 kuma Garnet da Ruby sune mafi kasa na ma’adanain da aka samar a shekarar 2018.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!