Connect with us

MANYAN LABARAI

Obasanjo Ya Yaba Da Hukuncin Kotu A Kan Zaben Jihar Osun

Published

on

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya taya Sanata Ademola Adeleke, murna a kan nasarar da ya samu a kotun sauraron karan zaben gwamna ta Jihar Osun, a ranar Juma’a,a Abuja.
Cikin sanarwar da ya fitar a Abeokuta, ranar Asabar, Obasanjo ya yabawa Adeleke, a kan halin kirkin da ya nuna na zuwa kotu domin neman gaskiya.
Ya kwatanta shawarar da dan takaran na Jam’iyyar ta PDP ya yanke na zuwa kotu a matsayin shawarar da ta dace ga tsarin dimokuradiyya.
“Tilas ne a karfafa zuwa kotu, ba a raunana masu nufin zuwa ba, kamar yanda wasu mutane suke da nufin yi.
“A lokacin da na kame bakina a kan furta wani abu kan zaben 2019, saboda daya daga cikin jam’iyyun ta tafi kotu.
“Nijeriya ta ‘yan Nijeriya ne bakidaya. Za mu ci gaba da girmama wadanda suka aminta da duk wani abu mai kyau a matsayin mai kyau ga Nijeriya.
A cewar Obasanjo, kotu ma wani yanki ne na tsarin dimokuradiyya a Nijeriya, tilas ne kuma duk mai neman gaskiya ya nufi kotun.
Obasanjo ya kuma yabawa kotun a kan namijin kokarin da ta yi na warware abin da ta tabbatar da cewa ba gaskiya ne ba.
“Wannan aikin shi ne abu na farko da jami’an sashen na shari’a suka yi na dawo da martabar sashen na shari’a a daidai lokacin da ‘yan siyasa ke ta kokarin lalata sashen na shari’a.
“Kamar yanda na sha fadi ne, Duniya ta zuba ido ne a kan abin da ke faruwa a Nijeriya.
“Duk abin da muka yi, ko kuma wanda ba mu yi ba ta hanyar gaskiya a kan zabe, ba Nijeriya ne kadai zai shafa ba, zai iya shafan Afrika bakidaya, ko ma Duniya bakidayanta.
“Ta hanyar gyara abin da kowa ya san kokari ne na marasa kishi na ganin sun canza abin da jama’ar Jihar Osun suka zaba, kotun ta ceto Nijeriya daga aikata abin kunya, ta kuma fara shirin cetowa da karfafa tsarin dimokuradiyya.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!