Connect with us

RAHOTANNI

PDP Da Atiku Abubakar Sun Gabatar Da Hujjojin Tunbuke Shugaba Buhari A Kotu

Published

on

An fara samun wasu daga cikin bayanan hujjojin da suke cikin karar da aka shiga ranar Litinin, wanda jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar da kuma dantakarar ta na Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar inada yake kalubalantar nasarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu, a zaben Shugaban kasa wanda aka yi ranar 23. ga watan Fabrairu.
Ita dai karar da aka shigar ta dogara ne akan wasu takardun bayanai 50 da aka gabatar a gaban kotun sauraren kararrakin zabe wadda ke Abuja, inda ake karar Hukumar zabe mai zaman kanta, da kuma Buhari da kuma jam’iyyar gaba daya .
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ranar 27 ga watan Fabrairu 2019 ta bayyana Buhari a matsayin wanda ya samu nasara a zaben, inda ya samu kuri’u 15,191,847 ya kada Atiku wanda ya samu kuri’u 11,262,978 .
A cikin takardar karar wadda take da shafi 139 daga wasu bayanai na karar da karar da aka shigar Hukumar zabe mai zaman kanta tana daga cikin wadanda ake karar, ainihin sakamakon zaben Shugaban kasa shine kamar yadda ya nuna cewar Atiku ya samu yawan kuri’un da suka kai 18,356,732 wanda ya kada Buhari wanda ya samu kuri’u16,741,430.
Sun bayyana cewar su kuri’un sune wadanda ‘yan takarar biyu suka samu daga jihohi 35 da kuma Babban birnin tarayya, n tun da yake babu wani bayani dangane da sakamakon jihar Ribas ya zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu 25, 2019.
Da wannan kuma shi Atiku yake cewar ya kada Buhari da kuri’u milyan1,615, 302.
Daya dada bcikin hujjoji biyar da aka shigar da karar, ana nufin a nuna cewar shi Buhari bai ma cancanta ya tsaya takarar ba, ta ofishin Shugaban kasa, saboda kuwa bai samu mallakar shaidar takardar ilimi mafi kankanta ta ilimin kammala makarantar Sakandare.
Su dai hujjojin biyar sune kamar haka “ Wanda ake kara na 2 (Buhari) ba wai an zabe shi bane saboda shi bai samu kuri’u masu yawa ba wadanda aka jefa lokacin lokacin zabe.
“ Zaben da aka yi ma nma 2 abin bai dace ba saboda dalilan da suka shafi cin hanci da karbar rashawa da cin hanci.
“Shi zaben wanda aka yi ma na 2 abin bai dace ba saboda dalili na rashin bin ka’ida da dokokin zabe na shekra ta 2010 kamar dai yadda aka yi gyara.
“Shi wanda ake karar na 2 a lokacin da za’ayi zaben bai cancanta bay a tsaya takarar zabe.
“ Cewar shi mutumin na 2 ya gabatar da wata takarda ga na 1wasu bayanai wadanda suka kunshi abubuwa na bayanan karya, duk a wani kokarin da yake yi saboda ya kare al’amarin daya shafi ilimin daya ce ya mallaka.”
Da suka ci gaba da bayar da bayanai gaba sun ce Buhari bai cancanta ba ya tsaya takarar ofishin Shugaban kasa, haka dai su wadanda suka shigar da karar suka yi maganar cewar, bai mallaki takardar shedar ilimi wadda zata bashi dama ta ya tsaya takartar Shugaban kasa wanda zai Shugabanci al’ummar kasar Nijeriya.
“Wadanda suka shigar da karar suka bayyana cewar sashi na 31 sakin layi na (1) na dokokin zabe kamar yadda aka gyara na shekra ta 2010, ko waccec jam’iyyar siyasa cewar daga cikin kwanaki 60, kafin ranar da za ayi, da cewar, ko wacce jam’iyya ta aika da sunayen ‘yan takararta da take son su tsaya takara zabubbuka.
“ Hakanan idan aka dubi sashe na 31 sakin layi na (2) na dokar zabe ta shekarar 2010 kamar yadda aka yi mata gyara, cewar sunayen da aka mika na ‘yan takara, ko kuma duk wasu bayanai wadanda ko wanne dan takara ya bayar, dole ne ya kasance ya sa da wata takardar rantsuwa wanda shi dan takarar ya yi a kotun Babban birnin tarayya, Babbar kotun jiha, ko kuma ta Babban birnin tarayya, cewar duk ya cika ka’idojin da suka kamata na tsayawa zabe shiu ofishin daya ke son takarar.
“Shi mutumin na 2 ha cika da kuma maida ita takardar Form ta CF001 wadda zai kai ko kuma mai da ta kamar yadda ya dace. kamar dai yadda ya dace, zuwa ga kwamishinan rantsuwa R a ofishin Rajista na Babbar kotu ta babbar birnin tarayya Abuja ranar 8u ga watan Oktoba, 2018. Cewar ita takarda ta Form CF001 tana biye ne da wata takarda wadda take nuna cewar can amshi ita takardar.
“ Su wadanda suka shiga da karar sun bayyana cewar shi ko kuma ita takardar ta Form CF001 kamar dai yadda aka cika ta aka kuma mayar, wanda mutumin na 2 ya yi ya kuma maida ma na 1, saboda tsayawa takara ofishin Shugaban kasa ita takartdar an hada ta tare da bayanan shi mutumin na 2 har ma tare da wata babbar takarda,wadda shi mutumin na 2 ya cika a Babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, tare da katin shedar dan jam’iyya da kuma katin zabe.
“ Su bayanan da aka gabatar ma wadanda aka kai ma ita Hukuma wadda take ta 1 Hukumar zabe (INEC) wanda shi na 2 ya ke shi (Buhari) ke nan, cewar abin karaya ne, saboda kokarin da ake yi na taimaka ma ilimin da yace ya mallaka. Kuma ya yi rantsuwaa kotu cewar su bayana da ya gabatar gaskiya ne.: ‘Ina gaskata cewar duk bayanan dana bayar cikin wanan takarda, a iya sani na gaskiya ne, duk kuma wasu bayanan dana bayar duk gaskiya ne’.”
Sun bayyana cewar su makarantun da shi Buhari ya ce ya yi da kuma satifiket din day ace ya mallaka, wadanda suka shafi makarantar Elmantare ta Daura Daura da kuma Mai Aduaa tsakanin shekarun 1948 da kuma 1952, sai kuma makarantar Middle ta Katsina tsakanin 1953 da kuma 1956 ga kuma kwalejin lardi ta Katsina ( wadda ake kira yanzu Kwalejin gwamnati ta Katsina) tsakanin 1956da kuma 1961, aka kuma bayyana hakan wanda shi na biyu ya bayyana a takardar bayananrayuwar shi ta aiki da kuma makaranta, wadda ya hada ta da Form CF 001, duk ma basu taba faryuwa ba kamar dai su wadannan shekarun.”
Sun ci gaba da maganar cewar shi mutumin na 2 ya yi bayani a Form CF 001 bayan daya cika ya kuma maida ma Hukumar zabe mai zaman kanta, a shedara ta C, layi na 2, shafi na 3, a karkashin makarantar Sakandare inda aka rubuta “WASC,” wannan kuma karya ne, saboda ana cewar an mallaki ita shaidar takardar ilimin ce, bayan kuma ba wani shaidar takardar ilimi da ake kira WASC a shekarar 1961.
“Su wadanda suka gabatar da karar cewar shi na biyun 2 cewar a wancan lokacin da kuma wannan bai cancanta ba, ya tsaya takara ofishin Shugaban kasa na tarayyar Nijeriya.
“Hakanan su masu gabatar da karar suka bayar da bayanin cewar duk kri’un da aka sa ma na 2 da kuma na 3 ranar 23 ga watan Fabrairu 2019 lokacin zaben Shugaban kasa, kamar dai yadda na daya ya bayar da sanarwar ranar 27 ga watan Fabarairu 2019 na, su kuri’u ne wadanda aka jefa na 2 bai cancanci ya tsaya takarar zaben.”
Sunayen manyan Lauyoyi na kasa SAN 21 da kuma wau lauyoyi 18 sun kasance lokacin da aka gabatar ko kuma shigar da ita shari’ar.
Ita dai tawagar lauyoyin tana karkashin shugabancin Mista Liby Uzoukwu (SAN).
Su suna bukata ne da su manyan dalilan nasu cewakr ita kotun sauraren kararrakin zaben ta bayyana cewakr shi Buhari, ba an zabe shi bane akan yawancin kuri’un da aka jefa na gaskiya, kuma maganar da ita Hukumar zabe ta bayyana cewar shine wanda ya lashe zaben Shugaban kasa, wannan ma maganar wasa ce, don haka bai ma kamata ayi ta ba”.
Hakanan ma su suna bukatar cewar tun da dai shi Atiku shine wanda aka zaba, shine wanda ya kamata ace ya lashe zaben Shugaban kasar na Nijeriya, saboda shine wanda yafi samun kuri’u na gaskiya, wadanda aka kada lokacin zaben Shugaban kasa na 23 ga watan Fabrairu 2019, ga shi kuma duk ya cika su sharuddan da suka kamata da kuma cancanta.
Hakanan ma suna bukatar da cewar ita Hukumar zabe data ba wanda suke wakilta Atiku Abubakar cewar shiune wanda ya lashe zaben Shugaban kasa, don haka ya bashi satifiket \m,ai nuna cewar shine wanda ya yi nasara amatsayin Shugaban kasar Nijeriya.”.
Hakanan ma suna bukatar ita kotun sauraren karar data yanke hukunci cewar shi Buhari “ a daidai lokacin da aka yi zaben bai cancanta ya tsaya takara ba, bayann na kuma su bayanan da y aba Hukumar zabe na karya ne, ba wata kanshin gaskiya cikin su, musamman ma shedar takardar ilimin day ace ya mallaka wadda ya tsaya takarar da ita.”.
Su kuma babbar bukatar su ita ce idan duk aabubuwan da suke nema basu samu ba,. to ya dai kamata a soke shi zaben da aka yi ranar 23 ga wtan Fabrairu 2019, a kuma gabatar da wani sabo.”
Su wadanda suka shigar da karar sun dogara ne akan wasu muhimman takardu masu bayanai 50, wadanda su kuma ke bukatar da ita Hukumar zabe mai zaman kanta data kawo na ainihin wadanda take ajiye dasu.
Wasu daga cikin muhimman takardun sun hada da, “ wata takarda daga Hujkumar zabe mai lamba ta daya (INEC Form CF001) wanda ake rubuta sunan dan takara na 2 wato Buhari (duk wasu takardu wadanda aka rubuta sakamakon zabe da suka hada suma da dukkan nin (Form EC8 Series), EC8A, EC8B, EC8C, EC8D da kuma EC8E – sai kuma takardar sheda wato satiket na sake samun nasara; sai kuma kati mai nuna cewar mambobin jam’iyyar PDP; da kuma katin kada kuri’a wanda Hukumar zabe ta bada , da kuma duk wasu katunan wadanda suke sheda.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!