Connect with us

MANYAN LABARAI

PDP Ta Lashe Zaben Kujerar Shugaban Karamar Hukumar Kuje

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta shelanta dan takaran jam’iyyar PDP Abdullahi Sabo, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka sake a karamar hukumar Kuje, ta babban birnin Tarayya.
Farfesa Titus Ibekwe, babban jami’in zaben, wanda shi ne ya shelanta sakamakon zaben, ya ce, Sabo ya sami mafiya yawan kuri’u har 19,090, inda ya doke mai ci yanzun Abdullahi Galadima, na jam’iyyar APC, wanda ya sami kuri’u 15,187.
Sai dai, wasu ‘yan bangan siyasa sun yi kokarin tsarwatsa tattara sakamakon zaben a Robochi, amma nan take jami’an tsaro suka shawo kan al’amarin.
Magoya bayan Abdullahi Sabo, na jam’iyyar ta PDP sun yi tururuwa bisa tituna suna nuna farin cikinsu da nasarar da PDP ta samu a karamar hukumar ta Kuje.
Yusuf Dabo, Kakakin Abdullahi Sabo din, cewa ya yi, nasarar zaben da aka sake yi nasara ce ga daukacin al’ummar ta Kuje, da kuma Dimokuradiyya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!