Connect with us

RAHOTANNI

WHO Ta Nemi Karin Tallafin Kudi Don Kawo Karshen Cutar TB Zuwa 2030

Published

on

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira da abokan huldarta akan a ci gaba da bayar da tallafi na kudade da kuma kayayyakin aiki, wadanda za su taimaka ma ita Hukumar wajen kawo karshen annobar cutar Tarinfuka wanda aka fi sani da suna Tuberculosis (TB) nan da shekara ta 2030.
Dokta Matshidiso Moeti wanda ita ce Darektar Hukumar ta nahiyar Afirka, a cikin jawabin nata lokacin da ake bikin ranar “Tarin fuka ta duniya” shekarar, tya bayyana cewar da yake ana samun kulawar kasashen duniya dangane da ita cutar, sai ga shi karsashin ita cuta yana kara yin kasa, a wasu sassa na duniya kamar dai ykadda Hukumar ta bayannan.
Ta ci gaba da bayanin cewar duk da hakan har yanzun ba a samu cimma wancan gacin da ake da muradin yin hakan ba, na kawo karshen ita cutar , nan da shekara ta 2020.
Moeti ta bayyan cewar saboda acimma burin kawo karshen ita cutar nan da shekara 2030, wadda shekrar ce ake sa ran za ‘a cimma su muradan kawo karshen cutar, don haka ya kamata gwamantocin kasashen ya kamata su kara yawan kudaden da suke badawa,saboda a samu kawo karshen cutar.
“Tarin fuka ko kuma TB daga karshe da ia ya fara samun kulawar data kamata a siyasance, wannan kuma shine zai sa a iya cimma burin a kawo karshen shi kamar yadda aka amince nan da shekarar 2020 ko kuma gaba da shi hasashen.
Ta ci gaba da bayanin cewar “ Muna sa ran mu ji daga abokan huldar mu na kasa da kasa, saboda su ci gaba da samar mana taimako kudadce da kuma kayayyakin aiki, a cikin kokarin da ake yi na yakar ita cutar tarin fukar da kumasauran wasu cututtuka wadanda suka yi kama da ita..
“A matsayina na Darekta na shiyar Afirka, ina mai tabbatar maku da cewar ofishina, da kuma dukkan ma’akatan da suke karkasina, a duk fadin nahiyar, dacewar su yi aiki da gwamantoci, da kuma sauran wadanda suke taimakwa, saboda a samu kawo karshen cutarnan da shekrara ta 2030 ko kuma kafin zuwan shekarar ma haka nan.
“A shekarar 2018 rahoton kasashen duniya kamar dai yadda ita Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana,shi dai yadda al’amarin ciwon yadda yake addaba da yawa, abin yanzu ba kamar da bane, a kasashen duniya masu yawa, amma kuma ba kamar yadda ake tsammani ba, yadda aka e sa rai nan da shekara ta 2020.
“A nahiyar Afirka ita cutar ba kamar dai yadda kowa yake tsammani ba, yadda ake samun ja-da baya na yadda cutar take kassara al’umma, wanda kashi hudu ne na, ko wacce shekara, saboda akbin ya kasance na biyu, tsakanin wasu sassan duniya, wannan kuma daga 2013 zuwa 2017.
“Bugu da kari ma an samu raguwar yaduwar yadda cutar take, wanda abin ya kai kashi 4 zuwa 8 ko wacce shekara, kamar yadda al’amarin ya faru a kudancin Afirka, kamar Eswatini, Lesotho, Namibia, Afirka ta Kudu, Zambia da kuma Zimbabwe, wannan kuwa ya biyo bayan tsaikon da aka samu akan annobar cutar Kanjamau da kuma yadda aka kara fadada yadda ake kawo cikas akan cututtukan wajen magungunan su da aka samu ci gaban aikin su.
“Saboda a ci gaba da yin shi wannan, da akwai bukatar su wadannan al’amuran, shi mizanin da ake bukata sanya jari daga gwamnatocin kasashen duniya, saboda a kawo karshen ita cutar TB, abin kuma ya dace ya hada da kulawa da su masu cutar, kada ya kasance ana kyamar su, dole ne hakan ta karu. Saboda kuwa kuwa shi halin da ake ciki yanzu, an samu koma baya wajen mizanin da ake sa ran cimmawa wajen kawo karshen ita cutar, wannan yana nufin ke nan kamar dai ita shekarar da ake sa ran hakan zai iya yiyuwa, domin a samu cimma muradun ci gaba’. “ Bugu da kari kuma akwai bukatar ma samu a dauki wasu matakai wajen gano su matsalolin, a kuma cire su, wadanda suke kawo cikas dangane da kokarin da ake yi, tar da ma, fitar da wasu tsare- tsare ko kuma manfofi wadanda ake ganin ba sai an kashe kudade masu yawa ba sai kuma maganar kawo dauki.
Moeti ta bayar da shawara cewar yadda za ‘a taimaka wajen al’amuran taimakawa da kudade, a rika yin su al’amuran daga cikin gida, sai kuma yadda ake taimakawa al’amarin da yadda tallafi daga mizanin kula da lafiyar al’umma, wadanda ya kamata su kasance nagartattun maganin yaduwar ita cutar, yadda za ‘a bincika domina gano ko an kamu da ita cutar, samar da magunguna, da kuwa yadda za ‘a lura dasu wadanda suka kamu da ita cutar ba tare da wata tsangwama ba.
Ta ci gaba da bayanin cewar da akwai bukatar su Shugabannin siyasa da kuma gwamnatoci, da su samar da wasu tsare-tsare, da kuma wasu manufofi, saboda a dai samu hanyoyin da za’a kawo karshen ita cutar.
Kamar dai yadda shi darektan nahiyar ta Afirka su matakan sun hada da yin wasu tanaje – tanaje, wadanda za ayi amfani dasu wajen maganin duk wadansu matsalolin da sukan kawo cikas, wajen kokarin da ake yi na, yadda za’a hana yaduwar su cututtukan. A samu kawar da yiyuwar kamuwar wasu, bama kamar mutanen da tuni sun riga suna dauke da su cututtukan, kamar cuar Kanjamau da kuma shi Tarinfuka.
Har ila yau ta bayyana cewar nan da karshen shekarar 2030, da akwai a tabbatar da cewar, an samu cimma shi muradin da ita Hukumar lafiya ta duniya take bukatar a cimmawa na an yi wasu gwaje-gwajen da suka kamata akan duk wani zaton da ake yi na yiyuwar kamuwa ra cutar .
Hakanan ma ta kara jaddada bukatar a bullo da wani sabon mngani wanda ita Hukumar lafiya ta duniya ta amince da shi, da kuma magungunan da za a hada su wajen sha saboda maganin matsalar da ak samu dangane da ita cutar yadda za’a dace da ingantaccen maganin ta.
Kungiyoyi masu zaman kansu da kuma al’umma na wurare daban- daban, ya dace su dauki wasu matakai, wadanda kuma suka hada da taimakon yin gwaji da kuma, musamman wuraren da su wadanda suke fama da cutar suke zaune, a kuma bunkasa da kuma taimakon samar da duk wadansu abubuwan dak suke bukata don taimaka ma gwamnatoci a suma nasu kokarin da suke yi.
“A cikin sakon dana aika ranar Tarinfuka ta duniya a waccan shekarar data gabata, na yi kira da gwamnatoci da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, a ko wanne irin mataki, da suyi amfani da mukamin su wajen kawo karshen yaduwar cutar Tarinfuka a nahiyar Afirka.
“Bayan taron da Shugabannin duniya da kuma wasu tsare- tsare suka yi, da kuma Shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu, a taron da aka yi na majalisar dinkin duniya, lokacin da aka yi taron duniya na dangane da cutar Tarinfuka cikin watan Satumaba na shekarar 2018, dukkan masu ruwa da tsaki dangane da shi al’amarin suna sane da ccewar akwai bukatar a dauki wani matakin gaggawa dangane da bukatar a kawo karshen yaduwar ita annobar.
“A nahiyar Afirka cutar Tarinfuka wata babbar matsala ce wajen al’amarin daya shafi ci gaba wanda kuma hakan ya kan samar da matsalolin da basu misaltuwa ga mutane wadanda suka fama da ita cutar. Wannan kuma shine yake kawo cikas wajen tunanin cimma muradan ci gaba nan da shekara ta 2030.
Moeti ta kara bayyana cewar lokaci yayi wanda za ayi kokari wajen kawo karshen fama da wasu matsaloli, na wadanda suke dama da ita cutar, da kuma iyalansu.
Kamar dai yadda ta bayyana taken bikin tunawa da masu Tarinfuka ta wannan shekara ta 2019 “Lokaci ya yi”.
Darektan ya bayyana cewar wannan wata dama ce wadda za ‘a tattauna ci gaba da aka samu shekarun da suka wuce, sai kuma abubuwan dfa suka kamata a kara maida kaimi wajen tabbatar da an kawo karshen yaduwar ita cutar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!