Connect with us

KASASHEN WAJE

An Hallaka Mutane 13 A Afghanistan

Published

on

Wani hari ta sama da rundunar kawance karkashin jagorancin Amurka ta kai, ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 13 cikinsu har da kananan yara 10 a Afghanistan.

A watan Fabrairu da ya gabata ne kungiyar Taliban ta yi watsi da tayin tattaunawa da gwamnatin shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan, sai an bayyana cewa wakilan suka shiga tattaunawar zaman lafiya da wakilan gwamnatin Amurka.

Majalisar dinkin Duniya ta fitar da wadannan alkaluma, yayin da ake danganta harin da kasar Amurka, a matsayinta na mai jagorantar sojin kawance na Nato.

Sai dai idan aka yi tuni kamar dai yada masana suka hango cewa Rasha da Iran na kokarin janyo hankalin Taliban domin kulla dangantaka mai karfi, saboda matsayin su na ganin Amurka ta janye daukacin dakarun ta a cikin kasar ta Afghanistan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!