Connect with us

WASANNI

An Nunawa Wadansu ‘Yan Wasan Ingila Wariyar Launin Fata

Published

on

Rahotanni sun nuna cewa; ‘yan wasan Ingila, Raheem Sterling da Callum Hudson Odoi sun yi tir da matsalar nuna wariyar launin fata a wasan da Ingilar ta lallasa Montenegro da ci 5-1 a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2020.

 

A yayin wasan na jiya Litinin, an yi ta rera wakar nuna wariyar launin fata da zimmar muzantawa wadansu daga cikin ‘yan wasan na Ingila da suka hada da Danny Rose.

Kocin tawagar Ingila, Gareth Southgate ya ce; za su shigar da kara a gaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai kan wannan batu.

Southgate ya ce, ba za a amince da irin wannan dabi’ar ba, yayin da ya jaddada cewa, da kunnensa ya ji ana zagin Danny Rose.

Shima Hudson Odoi ya ce da kunnesa ya ji magoya bayan Montenegro na kukan birrai, yana mai cewa, bai kamata a rika samun irin wannan dabi’ar ba domin kuwa dukkansu daya suke.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!