Connect with us

LABARAI

Ba Zan Bar Barayin Gwamnatin Bauchi Su Arce Da Sisin Kwabo Ba, Inji Kauran Bauchi

Published

on

Dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya shaida cewar zai yi iyaka bakin kokarinsa wajen kyautata shugabanci da kuma share wa al’umman jihar Bauchi hawaye a bisa zabin da suka yi masa a matsayin gwamnansu.
Sanata Bala yana shaida hakan ne a ranar Lahadi bayan da aka ayyana sakamakon zaben cike gurbi da aka sake yi a wasu kananan hukumomin jihar Bauchi kan zaben gwamnan jihar a wani babban taron manema labaru da ya kira, Sanata Bala ya gode wa illahirin jama’an jihar Bauchi a bisa zabin nasa da suka yi da kuma basu cikakken alwashin cewar zai kyautata shugabanci da kuma kare musu hakkokinsu, “Kun yi naku saura namu. Cikin yardar Allah gwamnatin Sanata Bala Kauran Bauchi za ta yi kokarin kyautata shugabanci,” Inji shi.
A gefe guda kuma, Sanata Bala, ya gargadi gwamnatin jihar Bauchi da ke ci a yau da cewar su guje wa yin wadaka da dukiyar jihar ta Bauchi a kokarinsu na wawushe lalitar gwamnatin jihar bayan shan kaye da suka yi.
Sanata Bala, ya shaida cewar yanzu haka idonsa na kan kowace irin sisi da kwabon da ake cirewa a cikin lalitar gwamnatin jihar, “Mun ji labarin akwai shirin wawushe dukiyar gwamnatin jihar Bauchi. To, muna shaida wa gwamnatin da za ta fita da cewar ta bi a hankali domin ba za mu taba kyalewa muna gani ana wawushe wa talakawa dukiyarsu ba, yadda suka zabemu za mu yi kokarin kare musu hakkinsu da dukiyarsu,” Inji shi.
Kauran Bauchi wanda ya ce, al’umman Bauchi sun zabeshi ne a bisa kyakkyawar fatar da suke da shi a kansa, ya ce zai kuma yi dukkanin kokarin da ya dace domin yi musu mai kyau.
Sanata Bala Muhammad ya kuma shaida wa jama’an jihar cewar zai tabbatar da shigo da wadanda suka dace da kyautata aiki a cikin gwamnatinsa, “Mu bamu kulli wani mutum a ranmu ba, za mu yi aiki da kowa da kowa domin tabbatar da kyautata jihar, da zarar muka amshi gwamnati za mu yi kokarin daukaka darajar jihar Bauchi,” A cewar shi.
Sanata Bala, wanda tsohon Ministan Abuja ne, ya zargi gwamnatin jihar Bauchi da kokarin yashe lalitar gwamnatin jihar domin huce haushin rasa mulkin jihar da suka yi, ya sha alwashin kwato sisin kwabo da aka sace na jihar.
A cewar shi; “Muna da labarin cewar jami’an gwamnati suna nan suna kwashe lalitar gwamnatin jihar a dalilin za su bar gwamnati, to ina baku tabbacin cewar kowani mutum guda da ya saci sisin kwabo sai ya amayar, za mu dawo da dukkanin kudaden da aka sace wannan tilas ne,” inji shi.
Ya nuna kwarin guiwarsa da jinjinarsa a bisa kokarin hukumar zabe kan zaben gwamnan jihar, ya kuma shaida cewar zabe ne aka gudanar cikin ruwan sanyi ba tare da wasu tashin hankali ba, “Muna godiya wa Allah da jama’an jihar Bauchi, ina kira ga magoya bayana su fito kansu da kwarkwatarsu da su fito su nuna murnarsu amma ina kira ga magoya bayana kada a yi murnar huce haushi a yi murna cikin kwanciyar hankali, Allah ya ce ka gode masa kan ni’imar da ya maka,” A cewar shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!