Connect with us

RAHOTANNI

Bangaren Saraki Sun Fara Taron Samun Shugabancin Majalisar

Published

on

Akwai rashin kwanciyar hankali a jam’iyyar APC yayin da wasu jiga – jigai na majalisar dattawa, suka fara zargin cewar akwai wata tada kayar baya, da Shugaban majalisar mai barinn gado Bukola Saraki, cewar shine wanda zai taka rawa wajen wanda za ‘a zaba Shugaban majalisar.
Ian dai samu wani rahoto wanda yake nuna cewar Saraki yana son ya nuna cewar har yhanzu yana fada aji , a al’amarin siyasar Nijeriya, bayan da kuma ya fadi zaben majalisar dattawa na kujerarr Danmajalisar dattawa nan a Kwara ta tsakiya.
Wata majiya ta bayyana ma wakilin cewar , wani wanda baya son a bayyana suna shi, ya bayyana cewar Saraki ya shirya ya tsaya takarar Shugaban majalisar dattawa, idan da ace bai fadi zaben shi ba wanda kuma dantakarar jam’iyyar APC ne, Dokta Oloriegbe Ibrahim.
Majiyar tamu ya bayyana cewar, “Saraki wani babban mai fada aji ne, wanda yake da wata kungiya a majalisar dattawa, wadanda suka kunshi ‘yan jam’iyyar PDP da kuma wasu Sanatoci da kuma mabobi na jam’iyyar APC wadanda suka taimaka ma shi ya samu nasara a zabe ta taimakon ‘yan jam’iyyar PDP .
“Har yanzu dai yana aiki ne akan gyauron shekarar 2015, ta yadda ya samu mukamin Shugaban majalisar dattawa, yayin da kuma Sanata , Ike Ekweremadu, ya kasance mataimakin shi.”
Wani binciken da aka yi ya bayyana cewar su ‘yan jam’iyyar sun yi taro a cikin makon daya gabata a Maitama gidan Shugaban majalisar dattawa, inda wasu daga cikin Sanatocin PDP, sun yinalkawarin za su bayar da gudunmawa wadda zata samar da Shugaban majalisar.
Ita dai kungiyar kamar dai yadda shi binciken ya nuna sun shirya su yi aiki tare da wasu Sanatocin APC APC wadanda kuma amince da shawarar da aka bayar, wadda ta nuna a sa ‘yan PDP cikin wasu mukamai na Shugabancin majalisar . .
Majiyar ta ci gaba da bayanin ta dai kungiyar “ Kungiyar tana da wasu tsare-tsare wadanda ta kira suna suna A B da kuma C, akan yadda za a samu cin ita Kujerar ta Shugabann majalisar dattawa “.
“Kamar dai ita kungiyar ta ci gaba da bayani ta, shi tsarin na farko, shine wanda za a tsaida daya daga cikinsu ya yi takararar majalisar, koda kuwa su ‘yan jam’iyyar APC, za su gabatar da kansu agaban majalisa wajen tsayawa takarar.
“Idan kuma an samu matsala shi tsarin nasu na farko ya samu nasara, da zubin farkon, saboda ana son Sanata Danjuma Goje na jam’iyyar APC jihar Gombe ta sashen Arewa maso gabas) wanda kamar yadda suka ce su sun fi amincewa da shi, suna kuma ganin tare da shi za su samu mukamin mataimakin Shugaban majalisar dattawa.
“ Hara ila yau akwai wata makarkashiya ta 3 idan ta 1 da kuma 2 ba’a samu nasarararsu ba, shine sub a Sanata Ahmed Lawan, wadanda suma suke gani shi ma ta bangaren shi ba za su yi asarar damar .”
Akwai kuma wata majiya wadda ta bayyana cewar, “ Muna da Sanatoci 42 wadanda su a shirye suke . Muna son Sanatoci guda goma sha hudu 14 da jam’iyyar APC wadanda za su nuna cewar su ba su amince da dokar karba karba ba,na ita jamj’iyyar , don haka za su ba jam’iyyar PDP gudunmawa ko kuma goyon baya .
“ Ita jam’yyar APC ba zata sake ta kasance tana da ‘yan takara biyu ba, wadanda suke neman mukamain Shugaban majalisar dattawa, idan kuma sun yi hakan, jam’iyyar PDP it ace zata samu nasarar yin hakan , kodai kai tsaye, ko kuma su sa wani mutumi wanda aka farar -farar da jama’a.
“ Taron mu da muka yi a makon daya gabata an yi shine saboda a tabbatar da mu rika yin wasu,saboda hakan zai sa asan muna cikin majalisar ta 9 abubuwa.”
Duk wani kokarin da aka rika y na samun maganar shi ta hanayar maiba shi shawara akan harkokin watsa labarai, abin ya ci tura, Yusuf Olaniyonu ranar Lahadi saboda kiran da aka uyi ta wayar shi, yaki shiga saboda duk wani kokarin da aka yi ba a samu cimma nasara ba .
Hakanan ma shi kokarin aikawa da sako ta waya shi saboda har yanzu ma ba a samu wata nasara ba.
Amma kuma suk da hakan shi Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewar zai tsaya takarar neman Shugabancin majalisar dattawa, ya bayyana hakan,a wata ganawa da yayi da manema labarai, cewar zai tsaya takarar, kuma abokan shi za su yi hadiun kai, domin tabbatar da cewar jam’iyyar APC ce ta karbi Shugabancin majalisar na tara..
Lawan kara bayyana cewar, “Mun koyi darussan mu a matsayinmu na jam’iyya, ina jin shi al’amarin Shugabancin majalisar dattawan, za ‘a bashi mhuhimmancin daya kamata, saboda a samu tabbatar da su majalisun biyu, sun samu Shugabanci, wanda zai yi ma kowa amfani.
“Yawancin mu a jam’iyyar APC muna jin cewar a wannan lokaci zamu saurari dukkan shawarwarin da za a bamu, da kuma yadda ita jam’iyyar take son ayi.
“Bana jin da akwai wani dan majalisar dattawa daya wanda zai kawo wani abin da zai kawo cikas akan tafiyar da ake shirin yi, muna kuma jin wannan lokaci jam’iyyarmu zata fito da wasu shawarwarin ita jam’iyyar, da kuma yadda za azabi su Shugabanni majalisa ta 9.
“ Muna jiran mambobin jam’iyya da masu son ci gaba su bi abubuwan da Shugabannin su suka fada masu, cewar su bi abubuwan da take son ayi.
“Ina ganin cewar jam’iyyarmu da Shugabanninmu cewar za su maida hankalin su ga Shugabancin na majalisun guda biyu, yadda za a samar dasu, dak zarar an kammala zabubbukan raba gardama.
“Ba zamu taba mantawa ba da cikin sauri akan irin halin da muka shiga ba, cikin shekaru hudu da suka .”
Sai dai kuma duk wani kokarin da aka yi naaji ta bakin Sanata Danjuma Goje abin ba a’a samu nasara ba, ranar Lahadi, saboda kiran wayar shi da aka ya yin da kuma har yanzu bai bada amsa ba, daga sakon da aka aika ma shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!